Zaman ɗari ɗari: Yan sanda sun kashe mutane biyu a Kano

Zaman ɗari ɗari: Yan sanda sun kashe mutane biyu a Kano

- Ana zaman dari dari a Kano bayan an zargi yan sanda da kashe wasu matasa biyu a unguwar Sharada

- Rahoto ya nuna cewa lamarin ya afku ne a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba lokacin da yan sanda da ke yaki da yan daba suka isa unguwar

- Zuwa yanzu dai mahukunta basu yi tsokaci ko fitar da jawabi a kan lamarin ba

An shiga halin fargaba a jihar Kano bayan kisan wasu mutane biyu da ake zargin yan sandan da ke yaki da yan daba a jihar da aikatawa.

Yayinda ba a fitar da kowani jawabi da ke tabbatar da hakan daga mahukunta ba, an tattaro cewa an harbe matasan ne a unguwar Sharada lokacin da sashin yaki da yan daba suka ziyarci yankin.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: ‘Yan bindiga sun sace malamin kwalejin Nuhu Bamalli da yara 2 a Zariya

Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya nuna cewa yan sandan kan matsa wa matasa a yankin amma sai aka samu tirjiya a wannan rana ta Asabar wanda ya yi sanadiyar bude wuta da mutuwar mutum biyu.

Zaman ɗari ɗari: Yan sanda sun kashe mutane biyu a Kano
Zaman ɗari ɗari: Yan sanda sun kashe mutane biyu a Kano Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Matasan da aka kashe sune Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman (Mainasara) jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar yan sandan jihar Kano bata riga ta yi martani a kan lamarin ba yayinda aka tattaro cewa an birne mutanen da aka kashe a ranar Lahadi.

A wani labarin, wani abun al'ajabi ya afku a birnin Makurdi,jihar Benue inda wani mutum mai matsaikatan shekaru ya cinnawa kansa da budurwarsa wuta.

Bayanai sun nuna cewa mutumin wanda har zuwa lokacin tattara wannan rahoton ba'a kai da gano kowaye ba, ya siyo fetur, ya kulle kansa a ɗaki tare da buduruwarsa a ciki kafin ya banka musu wuta gabaki ɗayansu.

Mutumin mai kimanin shekaru arba'in ya mutu sanadiyyar gobarar, inda ita ma budurwar tasa ta ƙone fiye da tsammani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel