Nasarun Minallah: Sojin Nigeria sun farmaki ISWAP, sun cafke masu haɗa makamin IEDs
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan yan ta'addan Boko Haram
- Sun dakile wasu hare-hare da yan ta'addan suka yi yunkurin kaddamarwa a yankin arewa maso gabashin kasar
- Sojojin sun kashe wasu daga cikin yan ta'addan sannan suka kama wasu masu kera bama-bamai
Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun Operation Fire Ball sun sha kan wasu yan ta’addan Boko Haram, sun kuma kama wasu daga cikin masu hada masu bama-bamai a yankin arewa maso gabas.
Mukaddashin daraktan labarai na tsaro, birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa dakarun da ke aiki karkashin Operation Lafiya Dole na ci gaba da aikin kakkaba don gano maboyar yan ta’addan.
Mista Onyeuko ya ce dakarun a ranar 11 ga watan Nuwamba, sun yi wani zazzafan fatrol domin kakkabe yan Boko Haram a mafakarsu da ke kauyen Ladantar a Borno bayan sun samu bayanai abun dogaro.
KU KARANTA KUMA: EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda
Ya ce dakarun sun fafata da yan ta’addan inda suka sha karfinsu wanda hakan ne ya sa su janyewa.
Ya ce dakarun sun kuma bi ta kan yan ta’addan da ke tserewa, sun kashe biyu sannan suka kama wani mai kera bama-bamai.
A cewarsa kayayyakin da suka kama sun hada da wani kwali na kayayyakin aiki da tukunyar gas wanda ake zargin da shine suke hada bama-bamai.
Mista Onyeuko ya bayyana cewa dakarun babban sansanin soji na 19 Bitta sun yi nasarar dakile harin yan ta’addan Boko Haram da suka yi kokarin shiga sansanin.
Ya bayyana cewa dakarun sun tursasa yan ta’addan janyewa sakamakon bude masu wuta da suka yi.
Ya kara da cewar dakarun birgediya 26 da aka tura Gwoza a ranar 8 ga watan Nuwamba, sun yi nazarin yan ta’adda da ke zuwa mabuyarsu a cikin wasu motocin bindigar toka hudu.
KU KARANTA KUMA: Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10
A cewarsa, dakarun sun fafata da miyagun inda suka kashe dan kunar bakin wake daya yayinda sauran suka tsere cikin rudani, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Dakarun bataliya 192 da aka tura Gwoza sun dakile wani hari da aka yi yunkurin kaiwa mabuyarsu a wannan rana.
'Yan ta'addan suna tafe ne a babura tare da shanu da tumakai a kauyukan Dankolo da Machitta da ke jihar Kaduna.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng