Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170

Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170

- Ba tare da bata lokaci ba, yan kasuwan mai sun yi tsokaci kan karin farashin mai

- Daga yau da yiwuwan gidajen mai su fara sayar da fetur N168 -N170

- IPMAN ta yi kira ga gwamnati ta tausayawa yan Najeriya ta dakatar da wannan kari

Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu (IPMAN) ta siffanta karin farashin Depot na man fetur daga 147.67 zuwa 155.75 ba tare da la'akarin irin halin kuncin da al'umma ke ciki ba.

Farashin Depot shine farashin da ake sayarwa yan kasuwan man fetur, sannan su sanya nasu farashin kafin sayarwa yan Najeriya.

IPMAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatad da wannan karin da hukumar NNPC ta sanar.

Shugaban kungiyar IPMAN, yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajudeen, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abeokuta, birnin jihar Ogun, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce kungiyar na rokon gwamnatin tarayya saboda gudun fushin jama'an kasar dake fuskantar matsalar tattalin arziki.

A cewarsa, wannan kari zai shafi kudin jigilar mai, kudin lodi, kuma gwamnati ba ta tunanin halin da yan kasuwa da al'ummar kasa ke ciki.

KU KARANTA: Gwamnatin Kogi ta sanya haraji kan kowane burodi a jihar

Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170
Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170 Hoto: NNPC
Asali: UGC

"Saboda haka muna rokon gwamnatin tarayya ta dakatad da karin har sai an samu saukin lamura," Tajudeen yace.

"Ba tare da tunanin halin da masu ruwa da tsaki ke ciki, gwamnatin tarayya ta sanar da sabon farashin da shugabannin NNPC suka ce za'a fara yau, Juma'a, 13 ga Nuwamba, 2002."

Ya bayyana cewa IPMAN za tayi ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki domin tattauna lamarin.

KU KARANTA: Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa

Mun kawo muku cewa yan Najeriya su shirya hauhawar farashin man fetur kwanan nan a fadin tarayya saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ta kara daga N147.67 zuwa N155.17, Premium Times ta ruwaito.

Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai.

A takardar da kamfanin ta saki ranar 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel