Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa

Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa

- Yan bindiga sun koma sace mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna

- Wannan karon abin ya rutsa shahrarren jarumin Kannywood, Ibrahim Maishinku

- Ya yi bayanin yadda ya tsallake rijiya da baya kuma aka sace abokinsa

Jarumi a masana'antar Kannywood, Ibrahim Maishinku, ya bayyana yadda ya tsallaka rijiya da baya yayinda yan bindiga masu garkuwa da mutane suka bude musu wuta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A jawabin da ya daura a shafinsa na Instagram, Maishinku ya bayyana cewa hakan ya faru da su da yammacin Talata bayan Sallar Magariba.

A cewarsa, yan bindiga sun kwashe kimanin mituna talatin suna bude musu wuta kuna sun yi awon gaba da abokinsa suna neman kudin fansa.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. A ranar Talata 03/10/2020 misalin karfe 7:16 na yamma na tsallake rijiya da baya sakamakon bude mana da wuta da akayi na sama da mintuna 30 a hanyar Abuja zuwa Kaduna, "yace.

"Hakan ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 10 yayinda aka sace abokinmu kuma dan uwanmu, Alh. Abdullahi Abubakar Wali, tare da wasu mutane 15."

"Dole na fada domin neman Addu'ar yan uwa sakamakon har yanzu yana hannun su don fansa. Allah ya takaitawa Abdullahi wahala, " ya kara.

KU KARANTA: Zamu fara bibiyan fina-finan Hausan a Youtube, Hukumar tace fim a Kano

Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa
Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa Credit: Maishinku/Facebook
Asali: Facebook

Bayan haka kuma, 'yan bindiga a jiya (Laraba) sun kashe matafiyi guda daya kuma sun yi garkuwa da wasu da dama a kusa da garin Rijana da ke babban titin Kaduna zuwa Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin Rijana, Ahmed Iliyasu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8.00 na safe a Gadar Malam Mamman da ke nisan kilomita kadan daga garin Rijana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel