Farashin man fetur zai tashi N170 yayinda aka kara kudin Depot zuwa N155
- Kuma dai, yan Najeriya zasu sake fuskantar karin man fetur a watan Nuwamba
- PPMC ta kara farashin Depot kuma hakan zai tayar da farashin da jama'a ke saya
Yan Najeriya su shirya hauhawar farashin man fetur kwanan nan a fadin tarayya saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ta kara daga N147.67 zuwa N155.17, Premium Times ta ruwaito.
Kamfanin PPMC wani sashe ne na kamfanin man feturin Najeriya NNPC, masu shigo da kusan dukkan man feturin da ake amfani a kasar nan.
Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai.
A takardar da kamfanin ta saki ranar 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.
Takardar da Ali Tijjani na PPMC ya rattafa hannu, ya nuna cewa kudin shigo da tattacan mai daga kasar waje ya hau daga N119 a Satumba zuwa N123 a Nuwamba.
Hakazalika, farashin mai a Depot ya tashi daga N138 a Satumba, zuwa N142 a Nuwamba, 2020.
Yanzu haka, farashin Depot ya tashi zuwa N155.17.
Farashin Depot shine farashin da ake sayarwa yan kasuwan man fetur, sannan su sanya nasu farashin kafin sayarwa yan Najeriya.
Saboda haka, fari daga 13 ga Nuwamba, da yiwuwan yan Najeriya su fara sayan mai a gidajen mai tsakanin N172 da N175, ko kuma fiye da haka.
KU DUBA: Zamu fara bibiyan fina-finan Hausa a Youtube, Hukumar tace fim a Kano
KU KARANTA: Yan bindiga sun budewa Ibrahim Maishinku wuta a hanyar Abuja-Kaduna, an sace abokinsa
A bangare guda, kamata ya yi ace ana sayar da litar man fetur akan N181, idan har za a yi la'akari da kudaden da ake kashewa wajen sarrafashi, mai makon N161 da ake sayar da shi yanzu, cewar FG.
Ministan cikin gida kan man fetur, Timipre Silver, ya bayyana hakan yana mai nuni da cewa Nigeria ta yi asarar N10.413trn daga 2006 zuwa 2019, a tallafin man fetur din.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng