An kai harin bam a wata maƙabarta a kasar Saudiyya

An kai harin bam a wata maƙabarta a kasar Saudiyya

- An kaddamar da harin bam a wata makabarta a Jidda, babbar birnin Saudiyya

- Lamarin ya afku ne a lokacin da jami’an diflomasiyya na kasashen waje suka taru domin ranar tunawa da mutanen da suka mutu a yakin duniya ta daya

- Kasar Faransa ta fito ta yi Allah-wadai da harin wanda aka kai a makabartar da ba na Musulmai ba

Rahotanni sun kawo cewa an kai harin bam wajen da jami’an diflomasiyya na kasashen waje suka hadu don ranar tunawa da mutanen da suka mutu a yakin duniya ta daya.

Lamarin wanda ya afku a birnin Jiddah ta kasar Saudiyya ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama.

A bisa ga wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin waje ta kasar Faransa, ta bayyana cewa bam din ya tashi ne a wata makabarta da ba ta Musulmi ba a yayin taron tunawa da mamatan, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

An kai harin bam a wata maƙabarta a kasar Saudiyya
An kai harin bam a wata maƙabarta a kasar Saudiyya Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Faransa ta yi Allah-wadai da lamarin wanda ta kira da “harin da matsorata suka kai da baya bisa ka’ida.”

KU KARANTA KUMA: Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai

An tattaro cewa har yanzu hukumomin Saudiyya ba su ce uffan ba game da harin.

A wani wallafa da wata yar jarida mazauniyar Saudiyya, Clarence Rodriguez ta yi a shafin Twitter, an gano hotunan yadda aka kai harin na yau Laraba, inda aka nuna yadda ake bai wa wani da ya ji rauni agaji.

KU KARANTA KUMA: Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu

"An kai wani hari makabartar da ba ta Musulmai ba da safiyar yau a Jiddah.

"An raunata mutum...[13] kwanaki kaɗan bayan harin wuƙa da aka kai a ofishin jakanci, an sake kai wa Faransa hari?" fassaran rubutunta.

Ta kara da cewa wani jami'in tsaro dan kasar Girka wanda bai saka kayan sarki ba ya ji rauni sosai. Ta ce tuni aka kai shi ofishin jakadancin Girka.

Wani jami'in jakadancin Girka ya bayyana cewa mutum hudu sun samu rauni a yayin harin, ɗaya daga ciki kuma dan asalin kasar Girka ne.

Ma'ikatar harkokin waje ta Saudiyya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da "ta yi karin haske kan wannan harin, tare da ganowa da kuma ɗaukar mataki kan waɗanda suka kai harin".

A gefe guda, kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa wasu dokokin shari’ar Musuluncin kasar gyaran fuska, inda a yanzu ta halasta shan giya da zaman dadiro.

Wannan kwaskwarima da kasar ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ta ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng