Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai

Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai

- Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ya mika ta'aziyyarsa a kan mutuwar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Balarabe Musa

- El-Rufai ya ce jihar Kaduna na alfahari da marigayin kuma za a dunga tunawa da shi saboda gudunmawar da ya ba jihar da Najeriya

- Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin kasa domin tabbatar da damokradiyya da adalci ga talakawa

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnatinsa na matukar alfahari da aikin da Alhaji Balarabe Musa, gwamnan tsohuwar Kaduna ya yi wa jihar da mutanenta.

A wani jawabi da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Mista Muyiwa Adekeye ya saki a ranar Laraba, ya bayyana cewa ya aika sakon ta’aziyyarsa zuwa ga iyalan Alhaji Balarabe, biyo bayan rasuwar tsohon gwamnan.

El-Rufai ya bayyana cewa “za a dunga tunawa da Alhaji Balarabe Musa a matsayin nagartaccen dan siyasa wanda a lokacin da yayi gwamna ya yi kokarin samawa talakawa damammaki.”

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Yan daba sun farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu

Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai
Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai Hoto: @DailyPostNGR/@vanguardngrnews
Asali: Twitter

A cewar gwamnan, marigayin “ya bayar da gagarumin gudunmawa wajen azurta jihar da masana’antu.

“A matsayinsa na shugaba, ya nuna bajinta, da ikon jam’iyyar siyasa da ke muradin kare ra’ayin talakawa domin samar da mulki bisa tafarkin damokradiyya.

El-Rufai ya yi nuni ga cewa: “a matsayinsa na dan kasa mai zaman kansa, ya kimanta ingancin manufar siyasa, mutunci, daidaito da kuma jajircewa don inganta rayukan talakawanmu a jihar Kaduna da Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu

“Duk da lamuran da suka kai ga tsige shi daga ofishin gwamna, Alhaji Balarabe Musa ya ci gaba da jajircewa a kan manufofinsa da kuma fadar ra’ayinsa a koda yaushe, fitowa wajen nuna kishin kasa a bainar jama’a domin kare damokradiyya, da kuma inganta adalci a cikin mutane."

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'azziyarsa ga iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, wanda ya rasu ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2020.

Buhari ya siffanta Balarabe Musa a matsayin jajirtacce wanda yayi yaki tukuru wajen tabbatuwar demokridayya a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng