Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu

Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu

- IGP Mohammed Adamu ya yi karar wani tsohon mataimakin gwamnan Imo, Ikedioha Ohakim a gaban wata babbar kotun FCT

- An gurfanar da Ohakim a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, kan zargin yada labaran karya

- Sai dai kuma ya ki amsa tuhumar da ake masa, an ba tsohon gwamnan beli na naira miliyan 10

A ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedioha Ohakim, a gaban wata babbar kotu a birnin tarayya kan zargin bayar da bayanan karya.

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja.

Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu
Saboda yaɗa labarin ƙarya: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Sai dai kuma, mai alkalin da ke jagorantar shari’a, Justis Samira Bature, ta bayar da belin tsohon gwamnan kan naira miliyan 10 bayan ya ki amsa laifinsa, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar

An bayar da belin nasa ne a matsayin amsa ga ikirarin lauyan Ohakim, K.C.O Njemanze, wanda ya yi ikirarin cewa tuhume-tuhumen da ake yiwa wanda yake karewa na iya samun beli, matsayar da lauyan mai kara, Stanley Nwodo ya yi adawa da shi.

A wani labarin, wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba a majalisar wakilai, Mista Victor Mela, bisa zarginsa da bayar da bayanan karya ga hukumar zabe ta kasa (INEC) tare da yin rantsuwa a kan cewa gaskiya ne.

Kotun ta ce dan majalisa Mela, mai wakilatar mazabar Billiri/Balanga a majalisar tarayya, ya bawa INEC bayanan karya domin samun damar tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

Hukumar 'yan sandan birnin tarayya (FCT), Abuja, ce ta gurfanar da Mista Mela bayan zarginsa da rattaba hannu, a matsayin rantsuwa, a kan bayanana karya da ya bayar yayin cike fom din hukumar INEC mai lamba CF001 gabanin zaben 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng