An yi wa shari'ar Musulunci kwakwarima a UAE, an halasta shan giya da zaman dadiro

An yi wa shari'ar Musulunci kwakwarima a UAE, an halasta shan giya da zaman dadiro

- Kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa shari'ar Musulunci kwakwarima

- A yanzu an halasta shan giya da zaman dadiro sabanin yadda ake a baya a kasar

- Hakan ya biyo bayan kokarin da kasar ke yi na habbaka tattalin arzikinta tare da jan hankulan masu zuwa yawon bude ido

A kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasarta da zamantakewa, kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa wasu dokokin shari’ar Musuluncin kasar gyaran fuska, inda a yanzu ta halasta shan giya da zaman dadiro.

Wannan kwaskwarima da kasar ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ta ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

A ganin UAE hakan da ta yi zai habbaka tattalin arzikinta tare da nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai sassaucin ra’ayi, karbar sauyi da kuma tafiya da zamani.

Wannan yunkuri ya biyo bayan wata yarjejeniya mai cike da tarihi da kasar ta dauka domin dawo da hulda tsakanin UAE da kasar Isra’ila, wacce ita ma ake sa ran za ta kara yawan masu yawon bude ido da zuba hannun jari.

KU KARANTA KUMA: Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed

An yi wa shari'ar Musulunci kwakwarima a UAE, an halasta shan giya da zaman dadiro
An yi wa shari'ar Musulunci kwakwarima a UAE, an halasta shan giya da zaman dadiro Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Hakazalika lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da gagarumin taro na World Expo.

An shirya gudanar da babban taron wanda ake sanya ran zai kawo harkokin kasuwanci masu tarin yawa da kuma baki kimanin miliyan 25 cikin kasar, ne a watan Oktoba.

Amma kuma sai aka samu tsaiko saboda annobar korona.

Kasar wacce ke samun kaso biyar na kudaden shigarta daga masu yawon bude ido ta samu tarnaki sakamakon dokar kulle na duniya da kuma hana jiragen sama jigila.

Sabon sauyin ya soke hukuncin da aka tanadar wa masu shan giya, sayenta ko mallakarta ga ’yan shekara 21 zuwa sama.

Ko da yake ana samun giya kusan a dukkan mashaya da wuraren shakatawar biranen kasar, a baya mutane na bukatar lasisin gwamnati domin sayarwa, jigila ko kuma shanta.

Sabuwar dokar za ta kyale Musulmai wadanda a baya aka haramta wa mallakar lasisin giya su iya shan giya ba tare da wani matsala ba.

KU KARANTA KUMA: Mahmood Yakubu: Shugaban INEC ya ce ci gaba da zama a kujerarsa zai zama ba daidai ba

Har ila yau dokar ta halastawa marasa aure su ci gaba da mu’amalar auratayya da juna jaridar The Guardian ta ruwaito.

Sai dai kuma sauran dokokin Musulunci za su ci gaba da kasancewa a dukkannin yankuna bakwai da suka hada Daular.

A wani labarin, wani ministan daular Larabawa, UAE, Anwar Gargash, ya bukaci al’umman Musulmi da su amince da matsayar Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.

Yana martani ne kan furucin Macron da ke cewar akwai bukatar addinin Musulunci ya tafi da tsarin zamantakewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel