Wata sabuwa: Yan daba sun kai farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu

Wata sabuwa: Yan daba sun kai farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu

- Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kai kan ofishin yan sanda a jihar Edo

- An tattaro cewa an aiwatar da aika-aikan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba

- A cewar rahoton, rundunar yan sandan ta dakile harin sannan ta kashe yan bindiga biyu

Wani rahoto daga jaridar This Day ya nuna cewa akalla mutane biyu ne ake zaton sun mutu lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari ofishin yan sanda a yankin Igueben, karamar hukumar Igueben na jihar Edo.

Legit.ng ta tattaro cewa yan bindigan wadanda suka aiwatar da harin a daren ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, sun kuma tsere da makamai da harsasai.

Kafin afkuwar lamarin, an rahoto cewa yan bindiga sun yi awon gaba da Fedrick Shaibu, dan uwan mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar

Wata sabuwa: Yan daba sun farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu
Wata sabuwa: Yan daba sun farmaki ofishin ƴan sanda, mutane 2 sun mutu Hoto: Businessamlive
Asali: UGC

Jaridar ta ce an kashe wani Inspekta na yan sanda da wani karamin jami’i a yayin harin yayinda wasu da dama suka jikkata.

An tattaro cewa maharan sun kai mamaya ofishin yan sandan da misalin karfe 8:00 na dare, suka jefa nakiya a harabar kafin suka iya shiga.

KU KARANTA KUMA: Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg

A bisa rahoton, harin ya haddasa gagarumar zanga zanga a yankin yayinda matasa suka fito unguwanni domin kira ga gwamnati a kan ta binciki lamarin.

Da yake martani, kakakin yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor ya karyata batun mutuwar jami’an yan sandan biyu.

Nwabuzor ya ce:

“A ranar 9 ga watan Nuwamban 2020, da misalin karfe 19.30hrs, wasu yan iska da ake zaton masu fashi da makami ne sun kai mamaya ofishin yan sanda a Igueben. Nan take, yan sandan suka dakile su.”

A wani labari na daban, a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedioha Ohakim, a gaban wata babbar kotu a birnin tarayya kan zargin bayar da bayanan karya.

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng