Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg

Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg

- Hukumar NDLEA ta damke mutane 92 da take zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano

- NDLEA ta samu wannan gagarumin nasara ne a cikin watan Oktoba

- Shugaban hukumar a Kano, Ibrahim Abdul, ya ce nauyin miyagun kwayoyin da aka kama a hannun mutun 92 din ya kai kilogram 987

Hukumar da ke kula da hana fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce ta kama wasu mutane 92 da ake zaton masu fataucin miyagun kwayoyi ne da kwayoyi da ya kai nauyin kilogram 987 a Kano cikin watan Oktoba.

Kwamandan hukumar a jihar, Dr Ibrahim Abdul, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a fadin birnin Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna, Balarabe Musa rasuwa

Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg
Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa farautar masu fataucin miyagun kwayoyin da hukumar ke yi bisa kudirin rage yawan fataucin kwayoyi da ta’ammali da shi a jihar na haifar da ‘ya’ya masu idanu.

“An gurfanar da mutum tara a gaban kotu, yayinda aka kai yan kwaya 101 bangaren gyaran hali, an tsare hudu, sai kuma biyu da aka sallama”, inji shi.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)

A wani labari na daban, rundunar Operation HADARIN DAJI da aka tura kauyen Dan-Ali, sun kama wani Jamilu Usman, wanda ake zargin ya hada kai da 'yan bindiga da ke karamar Hukumar Funtua a jihar Katsina.

Kakakin rundunar soji, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Litinin.

Yace yanzu haka wanda ake zargin yana hannun hukuma ana cigaba da bincike a kansa.

A cewarsa, an harbe 'yan bindiga 2 da ke ta'addanci a kauyen Fegi Baza da ke karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Hakan ya biyo bayan artabun da suka yi da sojoji, inda suka samu nasarar amsar bindiga daya, mashin daya da kuma wayoyi 2.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng