EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar

EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar

- Wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya dauki matakin doka a kan wasu yan Najeriya 50

- A karar da ya shigar, mai fafutukar kare hakkin dan adam din ya yi bayanin cewa ya kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga-zangar EndSARS

- Daga cikin wadanda aka yi kara akwai shahararrun mawaka, yan kwallon kafa, masu fafutukar kare yancin dan adam da kuma masu fada aji a soshiyal midiya

An maka yan Najeriya hamsin a bangarori daban-daban da suka hada da mawaki David Adeleke, jagorar #BringBackourGirls, Aisha Yesufu da kuma Fasto Sam Adeyemi a gaban kotun majistare da ke Abuja.

An kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga zangar EndSARS da aka yi kwanan nan.

A karar da wani mai fafutukar kare hakkin dan adam, Kenechukwu Okeke ya shigar, ya zargi wadanda ake karar da amfani da shafin Twitter wajen haifar da hargitsi da sunan zanga zangar EndSARS wanda daga bisani ya zama rikici.

Okeke ya ce aikin wadanda ake karar laifi ne da hukuncinsa yake a karkashin sashi na 97(2) na Penal Code Act, C53 dokar tarayyar Najeriya, 2004.

Ya wallafa a shafin Twitter:

“Bayan shigar da kara a kan wadanda suka bunkasa rikicin #EndSARS da karfe 1052hrs WAT, 09/11/2020, za mu tannatar da ganin cewa an hukuntasu saboda tsaro, da kuma kariyar jama’a.”

Tarayyar Najeriya kasa ce mai dokoki.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)

Legit.ng ta tattara jerin sunayen wadanda suka karfafa zanga zangar #EndSARS kamar yadda ta gani:

Aisha Yesufu

Oseni Etomi

Yemi Eberech Alade

David "Davido" Adeleke

Damini "burnaboy" Ogulu

EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar
EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar Hoto: Vanguard da sauransu
Asali: UGC

Kanu Nwankwo

Kiki Mordi

Peter Okoye

Paul Okoye

Deji Adeyanju

Tiwa Savage

Feyikemi Abudu

Debo Adebayo

Folarin "Falz" Falana

Maryam "Taoma" Akpaokagi

Dr. Joe Aba

Bankole Wellington

Uche Jombo Rodriguez

Ayo "AY" Makun

Japhet Omojuwa

Ikuforiji AbdulRahmon

Jola Ayeye

Laila Johnson-Salami

Anita "Tacha" Natacha Akide

Temitope Majekodunmi

Fakhriyyah Hasim

Oghenekaro Ibada Omu

Chbuzor Nelson

Ayo Sogunro

Pamilerin Adegoke

Chinedu Okoli

Micheal Collins Ajereh (Don Jazzy)

Yul Edochie

Ojabodu Ademola

Oduola Rinu

Tope Akinyode

Ogbeni Dipo

Small Doctor

Flavour

Agbelese Olamilekan

KU KARANTA KUMA: Maza ƙwaya, mata ƙwaya: NDLEA ta cafke mutane 92 da miyagun ƙwayoyi 987kg

Layo Ogunbanwo

Kelvin Shekahu

Runtown

Ibrahim Wizkid Balogun

Damilola Odufuwa

A gefe daya, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi gargadin cewa Najeriya na iya fuskantar sabuwar zanga zanga idan gwamnati ta gaza magance rashin aikin yi na matasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng