Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito

Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito

- Ahmed Musa ya wallafa hoton sabuwar motarsa kirar Benz Vito a shafin soshiyal midiya

- A yanzu haka shahararren dan kwallon na shirin buga wasa wanda Super Eagles za ta yi da Sierra Leone

- Musa ya buga wa kungiyar Super Eagles wasanni 93 tun 2010 inda ya jefa kwallaye 15 a raga

An gano kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa tare da sabuwar mota kirar Mercedes Benz Vito a kan hanya gabannin wasan shiga gasar cin kofin kasashen Afrika na 2021 da Najeriya za ta kara da Sierra Leone a Benin, Edo.

Tsohon dan wasan na kungiyar Kano Pillars ya je shafinsa na soshiyal midiya domin nuna wa masoyansa sabuwar motarsa bayan ya iso Najeriya gabannin babban wasan.

Ahmed Musa ya kasance daya daga cikin yan wasan Najeriya masu tarin kudi duba ga abunda tsohon dan kungiyar ta CSKA Moscow ya samu a duniyar kwallon kafa tun bayan da ya fara buga wasa.

A bisa ga dan gajeren bidiyon da Ahmed Musa ya wallafa, an gano dan wasan na Najeriya tsaye kusa da motar kirar Benz Vito baka cikin yanayi na farin ciki.

KU KARANTA KUMA: Za a iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya, Lawan ya yi gargadi

Musa ya kasance daya daga cikin yan wasa a duniya da ke son kasaitattun ababen hawa duba ga yawan motocin da ya mallaka a wajen ajiye motocinsa.

Ana sanya ran dan wasan mai shekaru 28 zai jagoranci Super Eagles a karawar da za ta yi da Sierra Leone a Benin a ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, a wasan shiga gasar AFCON.

KU KARANTA KUMA: Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito
Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito Hoto: ahmedmusa718
Asali: Instagram

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya yi ba’a ga gwamnatin tarayyar Najeriya a kan shirin ranto $1.2 biliyan na noma daga kasar Brazil.

Sani ya bayyana cewa neman rancen da Najeriya ke yi a wajen Brazil tamkar Ahmed Musa ke neman rance a wajen Neymar.

Musa ya kasance kyaftin a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, yayin dan gaba na PSG Neymar ya kasance kyaftin a kungiyar Samba Boys na Brazil.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel