Za a iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya, Lawan ya yi gargadi

Za a iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya, Lawan ya yi gargadi

- Sanata Ahmad Lawan ya yi gargadin cewa ana iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya

- Shugaban majalisar dattawan, ya ce mafita shine gwamnatin tarayya ta sama wa matasa aikin yi

- Ya bayyana hakan ne a yayin zaman kwamitin majalisar dattawa kan harkokin noma kan kasafin kudin 2021 na ma’aikatar noma

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi gargadin cewa Naeriya na iya fuskantar sabuwar zanga zanga idan gwamnati ta gaza magance rashin aikin yi na matasa.

Lawan ya yi gargadin ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, a yayin wani zama don kare kasafin kudin 2021 na ma’aikatar noma a majalisar dokokin tarayya.

Matasan Najeriya 10,000 ne suka gudanar da zanga zangar EndSARS a fadin kasar kwanan nan, inda suka nuna fushinsu a kan cin zarafin mutane da yan sanda ke yi da kuma rashin shugabanci nagari, lamari da ya ja hankalin gwamnati.

Lawan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakai a aikace wajen shigar da matasa a kasafin 2021, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

Za a iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya, Lawan ya yi gargadi
Za a iya fuskantar wata sabuwar zanga zangar ENDSARS a Najeriya, Lawan ya yi gargadi Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

“Ya kamata kasafin kudinmu na 2021 ya mayar da hankali ne wajen samar wa matasan Najeriya damar ayyukan yi.

“Sun gudanar da zanga-zanga saboda iya abun da za su iya yi ke nan, wasunsu kuma ba su iya shiga an yi da su ba amma suna tare da masu yi.

“Mu yi kokari mu same su a inda suke. Ba sai mun jira har sai sun yi kokarin zanga zanga ba. Mu dauki mataki. Mu isa garesu kuma suna a yankunan karkara ne. Mafi akasarinsu.

“Don haka mu same su a chan. Mu basu abunda za mu iya da kuma abunda suke bukata, wannan ita ce hanya daya tilo da za mu bi”, inji shi.

Shugaban Majalisar ya bayyana Ma’aikatar Noma ta Tarayya a matsayin wadda za ta kawo sauyi a Najeriya.

Ya ce ma’aikatar na da damar samar da ayyukan yi da bangaren mai ba zai iya samar wa mutane ba sai ‘yan tsiraru.

Ma’aikatar noma na da kasafin kudin naira biliyan 139 a 2021.

KU KARANTA KUMA: IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas

Amma Shugaban kwamitin majalisa kan noma, Abdullahi Adamu, ya ce kasafin kudin ya yi karanta sannan ya yi kira ga gwamnati da ta samar da manufofin da zai kawo sauyi a bangaren noma.

A gefe guda, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da matasan da ke zanga-zangar ENDSARS a kan cewa ganin damarsu ce su rungumi zaman lafiya.

Buhari ya yi wa matasa tunin cewa rayuwarsa da ta sauran sa'o'insa ta zo gangara, a saboda haka, zaman lafiya matasa zai fi yi wa rana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng