Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

- Ana rade-radin cewa gwamnan Ebonyi, David Umahi yana shirin komawa APC daga PDP a wannan makon

- Majiyoyi sun bayyana cewa tuni dai aka fara tattaunawa tsakanin Umahi da shugabannin APC a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja

- Ana zaton Umahi na zawarcin kujerar shugaban kasa ko na mataimakin shugaban kasa a zaben 2023

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi zai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Majiyoyi sun fada ma jaridar The Nation cewa Umahi na iya sanar da ficewarsa daga PDP, jam’iyyar da a cikinta ya lashe zaben gwamna sau biyu.

Jam’iyyar APC reshen jihar ta bugi kirji a ranar Lahadi game da shirin sauya shekar gwamnan, inda ta bayyana shi a matsayin ci gaba mai kyau.

An tattaro cewa Umahi na neman gurbi da zai cimma kudirin siyasarsa na gaba bayan cikar wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna na 2023.

Ana hasashen cewa gwamnan na hararar kujerar shugaban kasa ko na mataimakin Shugaban kasa a 2023.

Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon
Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

A ranar 19 ga watan Oktoba, mambobi 22 cikin 24 na majalisar dokokin jihar Ebonyi sun ba Shugaban PDP wa’adin kwanaki bakwai ya mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ga yankin kudu maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga

Kwana daya bayan haka, sai jam’iyyar PDP reshen jihar ta kuma bayar da wa’adi makamancin wannan ga Shugaban jam’iyyar na kasa kan bukatar mika wa kudu maso gabas shugabancin kasa na gaba.

APC ta shirya wa Umahi liyafa kamar yadda yake a cikin wata takardar yarjejeniya da aka saki a jiya Lahadi, a karshen wani taron masu ruwa da tsaki a Abakaliki.

Tsohon Shugaban karamar hukumar Ohaozara, Chaka Nweze, ne ya karanto takardar yarjejeniyar.

Sakataren APC a jihar, John Okochi, ya ce yana sane da tattaunawa a tsakanin Umahi da Shugaban jam’iyyar a Abuja.

Ya ce: “Ina sane da cewar akwai tattaunawa da ke gudana tsakanin gwamnan da hedkwatarmu a Abuja. Amma ban san fadin ko sun kammala tattaunawa ko basu kammala ba.

"Sai dai ina da tabbacin cewa da zaran sun gama, hedkwatar za ta sanar da sakatariyar jihar inda za ta sanar da mana da cewa mutum kaza ya zama dan cikinmu. Wannan zai bamu damar shirya masa liyafar maraba da zuwa."

KU KARANTA KUMA: Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS

Da aka tambaye shi ko da gaske Umahi ya yi rijista a matsayin dan APC a unguwarsa, ya amsa da: “Ba zan iya cewa ko yayi ba. Wannan lamari ne na unguwa ko karamar hukumarsa wacce take Ohaozara. A yanzu dai, sakatariyar jihar bata da masaniya.”

A wani labarin, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi zargin cewa masu daukaka zanga zangar EndSARS na so su yi amfani da shi ne wajen sauya gwamnati.

Dan majalisar a yayin wata hira da jaridar Daily Trust, ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan Najeriya ne ke daukar nauyin zanga zangar EndSARS domin kaskantar da arewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel