Musa na neman rance a wajen Neymar – Sani ya yi ba’a ga FG kan neman rancen $1.2b daga Brazil

Musa na neman rance a wajen Neymar – Sani ya yi ba’a ga FG kan neman rancen $1.2b daga Brazil

- Shehu Sani ya yi ba’a ga gwamnatin Najeriya a kan neman rance daga kasar Brazil

- Najeriya na neman sabon rance na $1.2 biliyan na noma daga kasar ta Kudancin Amurka

- Shehu ya bayyana lamarin da cewa tamkar Ahmed Musa ne ke neman rance daga hannun Neymar

Sanata Shehu Sani ya yi ba’a ga gwamnatin tarayyar Najeriya a kan shirin ranto $1.2 biliyan na noma daga kasar Brazil.

Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa kasar na neman kudi daga kasar ta Kudancin Amurka.

Ministar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta gurfana domin kare kasafin kudin ma’aikatar na 2021 a gaban kwamitin majalisar wakilai kan kudi.

A cewarta, gwamnatin tarayya ta gabatar da bukatar ciyo bashin zuwa majalisar dokokin tarayya wanda take shirin magance matsaloli dashi a fannin noma yayinda kasar ke yunkurin mayar da shi wani hanya na samun kudaden shiga.

KU KARANTA KUMA: Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai

Ta ce gwamnati na shirin samun fili hekta 100,000 a dukkanin jihohi 36 domin noman abinci.

A martaninsa, Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019, ya bayyana cewa neman rancen da Najeriya ke yi a wajen Brazil tamkar Ahmed Musa ke neman rance a wajen Neymar.

Musa na neman rance a wajen Neymar – Sani ya yi ba’a ga FG kan neman rancen $1.2b daga Brazil
Musa na neman rance a wajen Neymar – Sani ya yi ba’a ga FG kan neman rancen $1.2b daga Brazil Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Musa ya kasance kyaftin a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, yayin dan gaba na PSG Neymar ya kasance kyaftin a kungiyar Samba Boys na Brazil.

KU KARANTA KUMA: Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG

“Ahmed Musa na neman rance daga Neymar,” Shehu Sani ya wallafa a Twitter tare da kanen labarai ‘FG na neman sabon rance na $1.2bn daga Brazil.

A wani labari na daban, karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce an tura wa wasu malaman jami'an sama da asalin albashinsu, har wasu suka mayar wa da gwamnati kudinta, ChannelsTV ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng