Inda Najeriya da kasashen Afrika za su tsinci kansu karkashin mulkin Biden
A halin yanzu ana kokarin zaben shugaban kasar Amurka, kasashen Duniya sun sa idanu domin ganin yadda za ta kaya tsakanin Donald Trump da Joe Biden.
Jaridar Sahara Reporters ta yi fashin-baki game da yadda nasarar Joe Biden ko tazarcen shugaba Donald Trump za ta yi wa Najeriya da Nahiyar Afrika tasiri.
Wanda zai rike kujerar shugaban kasar Amurka ya na da tasiri a kan tattali da cigaban Afrika.
A karkashin Donald Trump, alakar Najeriya da kasar Amurka ta tabarbare. A 2019 gwamnatin Trump ta jefa Najeriya cikin kasashen da aka sa wa takunkumi.
Sauran kasashen da Trump ya sa wa takunkumi su ne: Myanmar, Sudan, Kyrgyzstan, Eritrea, da Tanzaniya.
KU KARANTA: Kanye West ya samu kuri’u daga jihohi 12 a Amurka
Bayan haka, gwamnatin Trump ta nuna tsantsar adawa ga mutumin Najeriya Akinwunmi Adesina, wwanda ke rike da kujerar bankin cigaban Afrika, AfDB.
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ita ce karshen wanda ta fuskanci kalubale daga gwamnatin Donald Trump. Amurka ta nuna ba ta goyon bayan takarar ta a WTO.
Ana sa ran cewa idan Joe Biden ya karbi mulki a Amurka, zai canza wasu muradu na Trump, daga ciki har da yarjejeniyar canjin yanayi da aka yi a Paris.
Biden zai yi kokarin tausasa wa musulmai, wanda Trump bai daukarsu tamkar sauran jama’a.
KU KARANTA: Jerin Jihohin da za ayi ta ta kare tsakanin Trump da Joe Biden
Daga cikin alkawuran da ‘dan takarar hamayyar, Joe Biden ya yi shi ne samun kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da kasashen Afrika da kungiyar AU ta Nahiyar.
Bayan haka, Biden ya sha alwashin dawo da tsarin takardun biza da damar aiki da kasar Amurka ta ke ba ‘yan kasar waje. Wannan zai rage matsalar zaman kashe-wando.
Biden a shafinsa, ya bayyana cewa gwamnatinsa zai jawo ‘yan ci-rani a jika a cikin kwanaki 100 na farko da zai yi a ofis. Akasin akidar shugaba mai-ci, Donald Trump.
Ana kyautata zaton Gwamnatin Biden kuma zai taimaka wa Afrika wajen yaki da ta’addanci.
A halin yanzu an yi kunnen doki a adadin Jihohi, amma Joe Biden ya ba Trump tazarar kuri’u
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng