Ragowar Jihohin da su ka rage a fitar da sakamako a zaben Shugaban Amurka
- Har yanzu ba a kammala fitar da sakamakon zaben shugaban Amurka ba
- Doka ta ba kowace Jiha damar daukan lokacin da za ta sanar da sakamako
- Pennsylvania, Arizona da Alaska na cikin jihohin da ake ganin akwai kura
Kamar dai yadda aka bayyana tun farko, wasu tsirarrun jihohi ne za su yi matukar tasiri wajen ganin wanda zai rike mulkin kasar Amurka nan da 2024.
Jihohin da kuri’unsu ke yin tasiri a Amurka su ne: Alaska, Arizona, Georgia, Michigan, Maine, Nevada, North Carolina, Pennsylvania da jihar Wisconsin
Daga cikin wadannan jihohi da ake ji da su a zaben Amurka, shugaban kasa Donald Trump mai neman tazarce ya yi nasara a Florida, Iowa, Ohio da Texas.
Alaska za ta fada hannun Donald Trump da gagarumar ratar kuri’u, yayin da ake maganar cewa Joe Biden ya yi galaba a kan Republican a jihar Arizona.
KU KARANTA: Trump ya na so a dakatar da kidayar kuri'u a zaben Amurka
Joe Biden shi ne ‘dan takarar Democrats na farko da ya yi nasara a Arizona tun shekarar 1996.
Shi kuma ‘dan takarar jam’iyyar hamayya, Joe Biden ya lashe New Hampshire da Minnesota.
A Amurka ba da kuri’un gama-gari ake zama shugaban kasa ba, akwai wasu mala’u da su ke kada kuri’u masu nauyin da su ke fito da wanda zai mulki kasar.
Hasashe ya nuna cewa jam’iyyar Democrats ce za ta yi nasara a jihohin Wisconsin da Michigan. Haka zalika Maine ta kubcewa shugaban kasa Donald Trump.
Ga dai jerin jihohin daya-bayan-daya:
KU KARANTA: Trump ya yi godiya ga mutanen garin Onitsha da su ka yi masa tattaki
1. Wisconsin
2. Michigan
3. Georgia
4. Arizona
5. Pennsylvania
6. Alaska
7. Nevada
8. North Carolina
9. Maine
Sakamakon zaben da aka yi a jihohin Nevada, Alaska da North Carolina zai iya daukar nan da zuwa ranakun Juma’a da Talata mai zuwa kafin su fito.
A ranar Laraba kun samu labari cewa Donald Trump ya fara kukan ana neman yi masa magudi a zaben Amurka, bayan ya hango nasararJam’iyyar Democrats.
Trump ya yi muhimmin jawabi bayan ikirararin Jam’iyyar Democrats su na yunkurin sace zabe.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng