Zaben Amurka: Tauraro Kanye West ya tashi da kuri’a fiye da 60, 000

Zaben Amurka: Tauraro Kanye West ya tashi da kuri’a fiye da 60, 000

- Kanye West ya samu kuri’u 60, 000 a zaben Shugaban kasar Amurka

- West ya tsaya takara a karkashin wata jam’iyya mai suna ‘Birthday’

- Mawakin ya nuna cewa zai sake jarraba sa’arsa da kyau a zaben 2024

Kanye West wanda ya sanar da cewa zai shiga takara a zaben Amurka na bana ya samu kuri’u duk da cewa ya janye wannan takara daga baya.

Mista Kanye West ya bada sanarwar zai yi takara ne a karkashin wata jam’iyya mai suna “Birthday Party”, daga baya kuma ya ce ya fasa takarar.

Jaridar Tribune ta ce duk da haka, Mawakin ya samu kuri’u fiye da 60, 000 daga jihohi 12 da aka sa sunan shi a cikin jerin ‘yan takara a zaben 2020.

KU KARANTA: Sakamakon zaben kasar Amurka kai-tsaye

West mai shekaru 43 fitaccen mawaki ne kuma mai fitowa a shiri a talabijin, shi ne ke auren taurariyar ‘yar wasar nan Misis Kim Kardashian.

Jaridar ta ce Jihohin da sunan Kanye West ya fito a cikin ‘yan takara su ne Arkansas, Colorado, Idaho, Iowa, Minnesota, Oklahoma, da jihar Utah.

Haka zalika sunansa ya fito a takardun kuri’un Tennessee, Kentucky, Louisiana da kuma Vermont.

RTE ta ce a karon farko, West ya yi zabe a Amurka, inda ya zabi kansa. Mawakin ya rubutu sunansa da kansa da ya ke kada kuri’a a Wyoming.

KU KARANTA: Trump ya na so a dakatar da kidayar kuri'u

Zaben Amurka: Tauraro Kanye West ya tashi da kuri’a fiye da 60, 000
Attajirin Mawaki Kanye West Hoto: www.rte.ie/entertainment/2020
Asali: UGC

West ya samu kuri’a mafi yawa har 10, 216 a jihar Tennessee. Mutane 4, 040 su ka zabi Kanye West a Arkansas, 6. 254 a jihar Colorado, 3, 631 a Idaho.

Haifaffen garin Atlanta a Georgia, West ya samu karin kuri’u kusan 23, 000 daga jihohin Minnesota, Mississippi, Oklahoma, Utah da Vermont.

Mutane 6, 259 da 4, 894 daga jihohin Kentucky da Louisiana su ka kada wa shahararren mawakin kuri’a. Tauraron ya ce zai sake takara a zabe na gaba.

Har ila yau, a game da zaben na Amurka, kun ji jerin Jihohin da za ayi ta ta kare tsakanin shugaba Donald Trump mai neman tazarce da kuma Joe Biden.

Kujerar Trump ta na lilo a hannun kuri’un mutanen Michigan da wasu Jihohi irinsu Nevada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel