Yadda sakamakon zaben Shugaban kasar Amurka ya ke ta cigaba da gudana
- Shugaban kasa Donald Trump ya na neman ya zarce a kan mulki a Amurka
- Zuwa yau ‘Dan takarar Jam’iyyar adawa, Joe Biden ya yi nasara a Jihohi 23
- Shi ma Donald Trump ya yi galaba a jihohi 23, ana jiran sakamakon jihohi 5
Yayin da ake cigaba da kidayar kuri’un da aka kada a Amurka, Aljazeera ta kawo jerin jihohin da jam’iyyar Democrats da Republican su ka yi nasara.
Kawo yanzu an raba kasar kusan biyu, inda wurare 23 su ka fada hannun shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican da abokin adawarsa, Joe Biden.
A safiyar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2020, Joe Biden ya na da kuri’u 71,515,822, hakan na nufin 50.28% na kuri’un da aka kirga sun fada hannunsa.
Shugaban kasa Donald Trump da jam’iyyarsa ta Republican suna da 48.1% na kuri’un da aka kidaya, da kuri’u 68,411,024, Joe Biden ya yi wa Trump nisa.
Ratar da ke tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da Trump ta haura miliyan 3.
KU KARANTA: Kujerar Donald Trump ta na lilo a kuri’un Jihohi 9
Haka zalika a kuri’u masu nauyi na ‘Electoral Collage’, Joe Biden ne ya ke kan gaba, da alamu ya na daf da samun 270 da ake bukata, inda Trump ya ke 214.
Ga yadda abin da ya ke:
Jihohin da Joe Biden ya yi nasara:
Arizona
Michigan
Minnesota
New Hampshire
Wisconsin
California
Colorado
Connecticut
DC
Delaware
Hawaii
Illinois
Maine
Maryland
Massachusetts
New Jersey
New Mexico
New York
Oregon
Rhode Island
Vermont
Virginia
Washington
KU KARANTA: Kanye West ya samu kuri’u daga jihohi 12 a Amurka bayan ya janye takara
Birane da jihohin da Trump ya lashe:
Florida
Iowa
Ohio
Alabama
Arkansas
Idaho
Indiana
Kansas
Kentucky
Louisiana
Mississippi
Missouri
Montana
Nebraska
North Dakota
Oklahoma
South Carolina
South Dakota
Tennessee
Texas
Utah
West Virginia
Wyoming
Ragowar inda ake jiran a kammala kidaya su ne:
Georgia
Nevada
North Carolina
Pennsylvania da
Alaska
Ba da dadewa ba aka samu labari cewa an tika Trump da kasa a jihar Michigan a zaben Amurkan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng