Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi
- Ministar kudi, Zainab Ahmed ta yi tsokaci kan yadda suka gaza wa yan Najeriya a matsayinsu na iyaye
- Zainab ta ja hankali iyaye ta bangaren sanya wa yayansu akidar sanin martabarsu domin ceto kasar daga hanyar durkushewa
- Ta kuma bayyana tanadin da gwamnatin tarayya ta yi wa matasan kasar ta hanyar samar da wani shiri na biliyoyin naira domin basu tallafi
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bukaci iyaye da su cusa wa yayansu akidar sanin martabobinsu a matsayin hanyar kare kasar daga durkushewa.
Ministar ta yi kiran ne a ranar Asabar, a Kaduna a yayin wani taro na masu da hakimai 77, Shugabannin addinai da na gari daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
“Mu na jan hankalin iyaye cewa mun gaza taɓuka komai wa yayanmu, duk martabobin da muke dasu a baya babu su a yanzu.
“Ya kamata mu tunatar da kanmu cewa akwai bukatar yaranmu su kasance a mike sannan cewa wannan ta’asar da ke gudana, a kullu yaumin ba zai amfane su ba kuma ba zai amfani jihar da kasar ba,” in ji ta.
KU KARANTA KUMA: An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)
Ministar ta yi godiya bisa kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi wajen kula da lamarin tsaro.
Ahmed ta fada ma masu ruwa da tsakin cewa gwamnatin tarayya ta samar da wani shirin tallafawa matasa na naira biliyan 75.
Ta ce an samar da shirin ne domin ba matasa a kasar damar habbaka kasuwancinsu da kuma dogaro da kai, jaridar Punch ta ruwaito.
Ministar ta yi bayanin cewa kudin zai tallafa wa matasan wajen sanin hazikancinsu da tunaninsu kan kasuwanci, zama masu amfani da kuma daukar wasu aiki.
Da yake magana a wajen taron, ministan muhalli, Dr. Muhammad Mahmud, ya yi kira ga hadin kai wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
KU KARANTA KUMA: Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olapade Agoro, ya rasu
Ya bukaci masu ruwa da tsaki a kan su tallafawa gwamnati wajen magance matsalolin tsaro da rashin aikin yi a kasar.
A wani labari na daban, tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.
Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng