Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da sarakunan gargajiyan Najeriya gaba daya
- Bayan ganawarsu da gwamnonin Arewacin Najeriya, Sarakunan gargajiya sun shiga tattaunawa da Buhari
- Buhari ya tattauna da su kan yadda gwamnati za ta amsa bukatun matasa
- Mai Alfarma Sultan na Sokoto ne ya jagorancin tawagar
Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka yana ganawa da wakilan sarakunan gargajiyan sassan Najeriya shida, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar.
Ganawar, dake faruwa a fadar shugaban kasa, Villa, Abuja ya samu hallaran Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi; Sarkin Kano, Etsu Nupe, Sarakunan yankin Igbo, dss, cewar Vanguard.
Shi ma Amanyanabo na kasar Twon-Brass, Mai martaba Alfred Diete-Spiff da wasu Sarakunan yankin Neja-Delta duk sun samu damar ganin shugaban kasar.
Duk da cewa ba'a san abubuwan da suke tattaunawa ba tukun, ana kyautata zaton yana da alaka da hadin kan kasa da kuma zanga-zangar EndSARS da akayi.
Kalli hotunan taron:
KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
KU KARANTA: Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta dena yin sulhu da 'yan bindiga
A wani labarin daban, a ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.
A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.
Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng