An kammala 80% a aikin matatar man Dangote da ake gina wa a Legas

An kammala 80% a aikin matatar man Dangote da ake gina wa a Legas

- Ana shirin karasa kamfanin taki da matatar man da Dangote ya ke gina wa

- Kamfanin takin zai fara aiki kwanan nan, a 2021 ne za a bude matatar man

- Darektan kamfanin ya ce annobar Coronavirus ce ta jawo masu cikas a aikin

Aikin matatar danyen man da kamfanin Dangote ya ke yi a Legas ya yi nisa, Daily Trust ta ce har an yi akalla 80% na wannan gagarumin aiki.

Ana sa ran cewa matatar ta soma aiki, a rika tace danyen mai daga tsakiyar shekara mai zuwa.

Bayan haka an kammala aikin kamfanin takin da Dangote ya ke gina wa. Kamfanin takin zamanin zai fara aiki ne a cikin watan Nuwamban nan.

KU KARANTA: Dangote da sauran Attajirai 7 da su ka fi kowa kudi a Afrika

Kamfanin takin ya na iya fitar da ton miliyan uku na takin zamanin Urea da Ammonia. Za a fara cin amfanin kamfanin nan da wasu kwanaki.

An kashe Dala biliyan biyu wajen gina wannan kamfanin takin zamani. Kamfanin da matatar su na yankin Lekki da Ibeju-Lekki ne a jihar Legas.

A ranar Laraba, babban darektan ayyuka na kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin, ya shaida wa ‘yan jarida inda aka kwana a wadannan ayyuka.

Matatar kawai za ta yi sanadiyyar samar da aiki ga mutane 240, 000 a karkashinta, bayan sauran kamfanonin Dangote da jama'a su ke neman abinci.

KU KARANTA: Gudumuwar Dangote ta sa Shugaba Buhari ya yaba masa

An kammala 80% a aikin matatar man Dangote da ake gina wa a Legas
Kamfanin Dangote Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Dangote ya shiga harkar mai duk da kazantar da ke ciki ne domin ya taimaki kasa, maimakon rijiyoyin mai, zai rika tace danyen mai ne inji Edwin.

Edwin ya ce: “Duk mun san darajar canji ya na lalace wa. A lokacin da na zo nan shekaru 29 da su ka wuce, ana saida Dalar Amurka ne a kan N10.”

Man da za a tace zai shiga kasuwa a 2021, Darektan ya kuma ce COVID-19 ya sa aikin ya samu cikas.

A Oktoban 2019 ne gidauniyar Aliko Dangote ta ba wa wasu mata kimanin 23,990 tallafin Naira miliyan 239.9 a jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya.

Dangote ya ce ya yi wannan ne domin inganta rayuwar al'umma, musamman mata da ke cikin kunci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel