Tafiya da Matasa zai taimaki Najeriya inji Ministar Abuja, Ramatu Aliyu

Tafiya da Matasa zai taimaki Najeriya inji Ministar Abuja, Ramatu Aliyu

- Karamar Ministar Birnin Tarayya ta na goyon bayan a dama da Matasa

- Ramatu Aliyu ta na ganin jawo masu jini a jika zai taimakawa kasar nan

- Ministar ta bayyana kokarin da gwamnatinsu ta ke yi na tafiya da matasa

Karamar ministar birnin tarayya Abuja, Dr. Ramatu Aliyu, ta bayyana cewa tsoma matasa a cikin sha’anin gwamnati shi ne zai kawo cigaba a Najeriya.

Dr. Ramatu Aliyu ta ce a dalilin sanin darajar matasa ne gwamnatin su a birnin tarayya Abuja, ta shigo da wasu tsare-tsare domin matasa masu jini a jika.

Da ta ke jawabi a garin Abuja, karamar Ministar tarayyar ta ce kwanan nan za a kaddamar da ayyukan.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar Nasarawa da ya ke faman jinya ya sauya-sheka daga PDP

The Guardian ta ce Ministar ta yi wannan bayani ne a wajen taron da shugabar wata kungiya ta matasan mata na Afrika, Dr. Jophia Gupar ta shirya jiya.

Wadanda su ka yi magana a taron sun hada da shugaban majalisar matasan Najeriya, Ango Suleiman da Zakari Babale na Conference for Patriotic Citizens.

Shugaban kungiyar of Uniform Voluntary Organisation, Muktar Akoshile da takwarorinsa Abraham Kwaghfan da Johnson Michael sun tofa albarkaci bakinsu.

Ministar birnin tarayyar kasar, Ramatu Aliyu, ta ce akwai bukatar a rika sa matasa wajen tsare-tsare da dabbaka manufofi da shirin da su ka shafi rayuwarsu.

KU KARANTA: Dangote ya ci karfin aikin matatar danyen mai a Legas

Tafiya da Matasa zai taimaki Najeriya inji Ministar Abuja, Ramatu Aliyu
Karamar Ministar Abuja, Ramatu Aliyu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Aliyu ta bada misali da irin kokarin da matasa su ka yi wajen raba kayan tallafin annobar COVID-19, inda su ka rika shiga sako-sako su na wannan aiki a Abuja.

Jaridar ta ce a wajen wannan zama, an yi magana game da abubuwan da su ka shafi samar da aikin yi, inganta tsaro, raya karkara da kuma gina tituna a gundumomi.

A jiya kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce kwamitin PTF ta ba Jihohin kasar nan N50bn kawo yanzu dmin a rika yi wa jama'a gwajin kwayar cutar Coronavirus.

Gwamnatin Buhari ta rabawa Gwamnoni 36 wannan makudan kudi ne a cikin watanni 10.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel