Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa

Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa

- Masu garkuwa da mutane sun saki alkalan kotun shari'a ta jihar Zamfara su biyu da suka sace

- Hakan na zuwa ne watanni biyu bayan sace su a hanyarsu ta dawowa Zamfara daga yankin Maradi a Jumhuriyar Nijar

- Sai dai an biya kudin fansar kowannensu naira miliyan daya-daya

An saki alkalan kotun shari’a biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara bayan an biya kudin fansa naira miliyan daya kowannensu, TVC News ta ruwaito.

Wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa da alkalan, Salihu Abdullahi da Shafi’u Jangebe kimanin watanni biyu da suka gabata, a hanyarsu ta komawa Zamfara daga Maradi a jumhuriyar Nijar.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: An haramta siyar da kayayyakin Faransa a Indonesia

An bukaci kowannensu ya biya naira miliyan 10, amma babu kudin. Daga bisani sai yan bindigan suka kira yan uwansu sannan suka bukaci da su biya duk abunda za su iya biya.

Daya daga cikin yan uwan alkalan da aka saki, Malam Hassan Samaru ya ce: “Da yan bindigan suka gano cewa ba za mu iya biyan abunda suka bukata ba na miliyan 20, sai suka kira mu sannan suka bukaci mu biya duk abunda muke da shi.

“Mun biya naira miliyan biyu na alkalan biyu sannan aka sake su,” in ji Mista Samaru.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka

Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa
Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sanda ta kama makasan dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Musa Baraza.

An kuma tattaro cewa an kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da Yaya Adamu, yayan gwamnan jihar.

An saki Adamu wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 25 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng