Batanci ga Annabi: An haramta siyar da kayayyakin Faransa a Indonesia

Batanci ga Annabi: An haramta siyar da kayayyakin Faransa a Indonesia

- Shaguna a kasar Indonesia sun dakatar da siyar da kayayyakin kasar Faransa

- Hakan mataki ne da suka dauka domin yin Allah-wadai da batancin da aka yi wa Annabi Muhammad a Faransa

- Sun ce sun gwammaci yin asarar dukiya a kan batancin da aka yi wa fiyayyen halitta

Rahotanni sun kawo cewa an haramta siyar da kayayyakin kasar Faransa a kasar Indonesia, hakan mataki ne na nuna bacin rai a kan kare zanen barkwanci da wata mujjalla ta yi kan Annabi Muhammadu (SAW)

Tuni dai wasu shagunan makarantar kwana a gabashiun ava da Yammacin Kalimantan mai suna "Basmalah Shop" ta yi umurnin cire duk wasu kayayyaki da yake na kasar Faransa a shagon, TRT Hausa ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka

Batanci ga Annabi: An haramta siyar da kayayyakin Faransa a Indonesia
Batanci ga Annabi: An haramta siyar da kayayyakin Faransa a Indonesia Hoto: @TRTHausa
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban shagon Basmalah Shop, Ahmad Edy Ami, ya bayyana cewa, "Mun dauki wannan matakin ne domin kalubalantar yunkurin tsokana da wulakanta Musulmi da Faransa ke yi, duk da hakan zai sanya mu rasa wasu kudade mun gwamacewa muyi hada kai da Musulmi domin yin Alla-wadai ga batancin da ake yi musu"

Shugaban Shura a yankin Kudancin Sulawesi, Muhammed Hiday Hanis, ya bayyana cewa shagunan yankin duk sun dakatar da siyar da kayayyakin Faransa a shagunansu.

KU KARANTA KUMA: Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi

A gefe guda, Sheikh Abdul Rahman Sudais, ya yi Allah-wadai da wadanda suka yi batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Sheikh Sudais, wanda ya kasance ministan Masallatai na kasar Saudiyya a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, ya nuna rashin jin dadi tare da yin kakkausar lafazi a kan masu aibata Annabi.

Shehin Malamin ya bayyana masu irin wannan danyen aiki a matsayin kaskantattun mutane marasa daraja da kima, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng