Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi

Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi

- Jami'an yan sanda sun yi nasarar damke makasan dan majalisar dokokin Bauchi, Musa Baraza

- Sun kuma kama wadanda suka yi garkuwa da yayan gwamnan jihar Bauchi, Yaya Adamu

- Gwamna Bala Mohammed ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba

Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sanda ta kama makasan dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Musa Baraza.

An kuma tattaro cewa an kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da Yaya Adamu, yayan gwamnan jihar.

An saki Adamu wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 25 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa ba za mu iya biya wa ASUU bukatarta ba - Ngige

Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi
Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Gwamna Bala Mohammed ne ya sanar da kamun masu laifin a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, lokacin da babban faston katolika na jihar Bauchi, Most Rev. Bishop Hilary Dachelem ya ziyarce shi a gidan gwamnatin Bauchi, babbar birnin jihar.

Wasu yan bindiga ne suka harbe Baraza wanda ke wakiltan mazabar Dass har lahira, a gidansa da ke Baraza a ranar 14 ga watan Agustan 2020.

Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da matansa biyu da yarsa mai shekara daya amma sai suka sake su daga bisani.

KU KARANTA KUMA: Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina

Mohammed ya ce: “Ina son amfani da wannan damar don bayyana cewa an kama dukkanin masu laifin kuma za su fuskanci hukunci,” in ji shi.

A wani labarin, mun ji cewa wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wata mata mai juna biyu a Kaduna a ranar Talata a unguwar Rigachikun.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ƴan bindigan sun sace matar ne tare da mijinta daga gidansu.

Majiyar ta ce wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kashe matar yayin da suke musayar wuta da jami'an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel