Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina

Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina

- Jami'an yan sanda a Katsina sun kashe wani kasurgumin dan fashi da makami

- Sun halaka dan ta'addan ne a wata fafatawa da suka yi da yan fashi a kan babban titin Bakori zuwa Kabomo

- Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da hakan ga manema labarai

Rundunar yan sandan Katsina ta halaka wani kasurgumin dan fashi a yayin wani fafatawa da suka yi a babban titin Bakori zuwa Kabomo a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa jami’an yan sanda a Bakori sun kai agaji ne a inda yan fashi suka tare hanya cikin dare, a nan ne suka halaka dan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya

Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina
Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya bayyana cewa: “da misalin karfe 8:30 na dare, wasu yan bindiga sun tare hanyar Bakori, sai dai mun yi nasarar dakile harinsu, sannan mun kashe daya daga cikinsu.

Gambo ya kara da cewa sauran yan ta’addan sun tsere, an kuma samu bindiga kirar hannu a wajen wanda aka halaka din.

Ya kuma ce tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano mafakar ragowar yan fashin.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa (hotuna)

A wani labari na daban, an ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wata mata mai juna biyu a Kaduna a ranar Talata a unguwar Rigachikun.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ƴan bindigan sun sace matar ne tare da mijinta daga gidansu.

Majiyar ta ce wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kashe matar yayin da suke musayar wuta da jami'an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng