Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa (hotuna)

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa ta kasa

- Taron na gudana ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a yau Laraba, 4 ga watan Nuwamba

- Mataimakin shugaban kasa, wasu manyan gwamnati da ministoci bakwai sun hallara yayinda sauran suka shiga taron ta yanar gizo daga ofishoshinsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa ta yanar gizo karo na 22, a yau Laraba, 4 ga watan Nuwamba, a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Taron wanda ke gudana a zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasa, ya samu halartan mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Ministoci bakwai da suka hallara sun hada da Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da Ministan Bunkasa Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare.

KU KARANTA KUMA: Musa na neman rance a wajen Neymar – Sani ya yi ba’a ga FG kan neman rancen $1.2b daga Brazil

Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa (hotuna)
Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Sauran sune Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Ministar Kudi, Zainab Ahmed.

Shugabar ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan da sauran ministoci sun halarci taron ne ta yanar gizo daga ofishoshinsu mabanbanta a Abuja.

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na Twitter.

Taron na gudana ne a a daidai lokacin da wa’adin mako guda da Buhari ya ba wa ministoci kowannensu ya kawo rahoton ganawarsa da jama’ar jiharsa ke cika.

KU KARANTA KUMA: Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG

A wani labarin, Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya jaddada biyayyar jami’an rundunar sojin Najeriya ga gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buratai ya bayyana matsayinsa ne yayin da yake jawabi a wajen bude taron rundunar sojin Najeriya na kwanaki biyu a Zaria, jihar Kaduna.

Shugaban sojin ya samu wakilcin kwamandan dakarun sojin kasar, Manjo Janar Stevenson Olabanji a taron, jaridar The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel