'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu sunyi garkuwa da mijinta a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu sunyi garkuwa da mijinta a Kaduna

- 'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun afka gida sun sace mata mai juna biyu da mijinta a Kaduna

- Matar mai juna biyu ta mutu sakamakon harbinta da 'yan bindigan suka yi yayin musayar wuta da 'yan sanda

- 'Yan bindigan sun yi nasarar yin awon gaba da mijin matar da suka sace yayin da ita kuma matar anyi mata jana'iza

An ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wata mata mai juna biyu a Kaduna a ranar Talata a unguwar Rigachikun.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ƴan bindigan sun sace matar ne tare da mijinta daga gidansu.

Majiyar ta ce wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kashe matar yayin da suke musayar wuta da jami'an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu sunyi garkuwa da mijinta a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu sunyi garkuwa da mijinta a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Har yanzu ba a gama samun cikakken bayani kan afkuwar lamarin ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige bai riga ya amsa tambayar da aka masa game da lamarin ba.

Amma majiyar ta ce, "Masu garkuwar sun afka gidan wadanda abin ya faru da su suka yi awon gaba da su, daga nan jami'an tsaro suka bi sahun su inda yayin musayar wuta masu garkuwar suka harbe matar kuma daga bisani ta mutu a asibiti.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama

"Matar na da juna biyu ta kusa haihuwa kafin abin ya faru. An mata jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci."

Masu garkuwar sun yi awon gaba da mijin.

A wani labarin, aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel