Nasarawa: John Osewu ya sauya-sheka, ya bar PDP ya koma Jam’iyyar APC
- John Osewu ya koma Majalisar Nasarawa bayan ya yi jinya na tsawon lokaci
- ‘Dan Majalisar ya bada sanarwar cewa ya bar PDP, ya koma jam’iyyar APC jiya
- Osewu ya ce ya yi haka ne bayan ya zauna da Gwamna da Shugaban Majalisa
Jaridar Vanguard ta ce John Osewu mai wakiltar mazabar Doma ta Kudu a majalisar dokokin jihar Nasarawa, ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP.
A jiya ranar Talata, Honarabul John Osewu wanda ya warke daga rashin lafiya ya bada sanarwar ya bar PDP, ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Nasarawa.
John Osewu ya bayyana haka jim kadan bayan ya koma bakin aikinsa a zauren majalisar Nasarawa.
KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Borno ya ce ya zabowa Jama'a Magajin da ya fi shi
“Lamarin rashin lafiya na ya galabaitar da ni. Ya sa na ji babu dadi. Wasu ma sun ce na mutu.” Inji ‘dan majalisar bayan ya dawo aiki a jiya da rana.
“Wasu sun ce shugaban majalisa ya boye ni, amma na gode wa Ubangiji, ga ni nan yanzu, tare da abokan aikina, ma’aikata da ku jama’a da ‘yan jarida.”
A jawabinsa, Osewu ya mika godiya ga mai girma gwamna Abdullahi Sule da kuma kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Balarabe Abdullahi.
Osewu ya ce gwamna Abdullahi Sule da Balarabe Abdullahi su ka ba shi shawarar ya koma APC, ya rabu da jam’iyyar da ta ba shi nasara a zaben 2019.
KU KARANTA: Minista ya ce alhakin yajin-aikin ASUU, ya na kan Gwamnatocin da su ka shude
“Ina so in sanar da ku cewa bayan na tattauna da mutanena, na bar PDP zuwa APC.” Inji Osewu.
Ya ce: “Na yi wannan ne domin in ba gwamna Sule cikakkiyar goyon-baya saboda ayyukan da ya ke yi wa mutane, irin wannan shugabanci ake so.”
Bayan nan kuma 'yan majalisar dokokin jihar Nasarawa sun dakatar da hadimin gwamna, Stanley Buba saboda zarginsa da ake yi da laifin rashawa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng