A kowane bangare, Gwamna Zulum ya fi ni inji Sanata Kashim Shettima

A kowane bangare, Gwamna Zulum ya fi ni inji Sanata Kashim Shettima

- Tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima ya gabatar da wata takarda a Kebbi

- Da ya ke jawabi, Shettima ya yabi aikin Magajinsa, Farfesa Babagana U. Zulum

- Farfesa Zulum ya yi aiki da Sanata Kashim Shettima a lokacin ya na gwamnati

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya yarda cewa babu shakka gwamna mai-ci, Farfesa Babagana Umara Zulum ya fi shi komai.

Daily Trust ta rahoto Sanata Kashim Shettima ya na cewa bai yi son-kai wajen zaben Babagana Umara Zulum a matsayin wanda zai gaje shi ba.

Shettima wanda yanzu haka Sanata ne ya bayyana wannan wajen wata lacca da ya yi a taron da wasu kungiyoyin matasa su ka shirya a jihar Kebbi.

KU KARANTA: Malamin Musulunci ya bayyana alheran Gwamna Zulum

Sanatan ya gabatar da takarda a wajen taron mai taken tasirin manyan Arewa wajen horas da matasa.

Kashim Shettima ya bada labarin irin tirka-tirkar da aka yi kafin a kai ga dauko Farfesa Babagana Umara Zulum domin ya yi takarar gwamna a Borno.

Tsohon gwamnan ya bayyana tsohon kwamishinansa, Umara Zulum da amintaccen ‘dan siyasa.

A cewar Shettima, gwamna na-yanzu, Farfesa Zulum ya fi shi komai. Ba wannan ne karon farko da 'dan siyasar ya fito ya na yabon tsohon yaronsa ba.

A kowane bangare, Gwamna Zulum ya fi ni inji Sanata Kashim Shettima
Gwamna Zulum da Sanata Kashim Shettima Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Diri ya yi wa Malaminsa godiya bayan ya zama Gwamnan jihar Bayelsa

“A matsayinmu na shugabanni, dole mu horas da matasa bakin kokarinmu, mu na sane da cewa ba za mu zauna har abada ba.” Inji tsohon gwamnan.

A takardarsa, Sanatan Borno ta-tsakiya, Shettima ya koka game da yadda mafi yawan matasa ba su da ilmi ko sanin aikin yadda za su juya taro ta zama sisi.

Kwanakin baya kun ji cewa Sanata Kashim Shettima ya yabawa gwamnatin Babagana Umara Zulum. Tsohon gwamnan ya yarda Magajinsa ya na aiki a Borno.

Zulum ya karasa wani aiki da aka bari, hakan ya sa Shettima ya roka masa gidan aljanna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng