Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa

Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa

- Gwamna Abdullahi Sule ya yanke shawarar yin sauye-sauye a majalisarsa

- Hakazalika majalisar dokokin jihar Nasarawar ta dakatar da hadimin gwamnan jihar, Stanley Buba saboda zargin rashawa

- Maalisar ta ce ta dakatar da Mista Buba domin bayar da damar yin bincike yadda ya kamata

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, yana shirin yin sauye-sauye a majalisarsa, biyo bayan zargin rashawa da ke yawo a wuyan wasu yan majalisarsa, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

An tattaro cewa a yan makonnin da suka gabata, majalisar dokokin jihar ta sammaci wasu manyan jami’an gwamnati a jihar.

An kuma rahoto cewa gwamnan zai gudanar da wani taro na musamman tare da wasu jami’an gwamnati domin neman mafita.

Har ila yau an tattaro cewa gwamnan zai yi gargadi ga wasu kwamishinoni a kan zarge-zarge mabanbanta a wajen taron.

KU KARANTA KUMA: Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa

Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa
Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa Hoto: Dailypost
Asali: UGC

Ku tuna cewa an kama babban mai ba gwamnan shawara na musamman a kan harkokin ci gaba, Arc. Stanley Buba, yana bayar da wasu umurni ba tare da bin dokar hukumar ci gaban birane na jihar Nasarawa (NUDB) ba.

Majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin mutum shida domin bincike a kan zargin rashawar.

Majalisar, karkashin jagorancin kakakinta, Ibrahim Balarabe ya kuma yi kira ga dakatar da Mista Buba domin bayar da damar yin bincike yadda ya kamata.

Balarabe ya bayyana cewa: “hukuncin da Majalisar ta dauka na cewa Stanley ya sauka daga matsayinsa ya kasance domin tabbatar da yin bincike kan ayyukan NUDB yadda ya kamata.”

Hakazalika, majalisar a watanni hudu da suka gabata ta yanke shawarar dakatar da babban sakataren gwamnatin jihar, Aliyu Tijjani kan zargin badakalar naira biliyan 1 na kwangilar ilimi.

Sauran jami’an gwamnati da majalisar ta bincika sun hada da shugaban karamar hukumar Nasarawa, Sani Ottos.

KU KARANT KUMA: 2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP

Har ila yau daga cikin wadanda aka bincika harda mataimakin shugaban karamar hukumar Karu, Lawan Karshi kan zargin rashawa.

Shugaban makarantun firamare na jihar, Muhammed Dan’Azumi ma ya gurfana a gaban kwamitin majalisar domin amsa tambayoyi kan kwangilolin makarantar firamare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel