Shugaba Trump ya na banbami, ya ce wasu sun yi zabe bayan lokaci ya kure

Shugaba Trump ya na banbami, ya ce wasu sun yi zabe bayan lokaci ya kure

- Donald Trump ya zargi Jam’iyyar hamayya da kokarin ‘sace zabe’

- Shugaban kasar ya ce wasu sun kada kuri’a bayan an rufe rumfuna

- Ana sa ran cewa an jima kadan Trump zai yi wa Amurkawa jawabi

Yayin da ake cigaba da sauraron sakamakon zaben shugaban kasa a Amurka, Donald Trump ya fito ya yi jifa da zargi mai karfi a ranar Laraba.

Donald Trump ya na zargin cewa ana kokarin sace masa kuri’u. Shugaban kasar bai bada wasu hujjoji da za su gaskata ikirarin da ya ke yi ba.

Shugaban ya ce an kyale wasu su na kada kuri’a a lokacin da ya kamata ace an rufe rumfuna.

KU KARANTA: Kuri'un sun fara fitowa a zaben Trump da Biden

Trump ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter, Legit.ng ta fahimci cewa Twitter ta yi wa wannan magana tambarin kanshin rashin gaskiya.

“Mu na gaba, amma su na kokarin sace zaben. Ba za mu taba bari su yi wannan ba.” Inji Trump.

‘Dan takarar jam’iyyar Republican din ya cigaba da cewa: “Ba za a rika kada kuri’a bayan an rufe rumfunan zabe ba.” - inji @realDonaldTrump.

Shugaban kasar Amurkan ya fasa wannan kwai ne da kimanin karfe 6:50 a agogon Najeriya. Twitter ta hana a iya maida martani a kan sakon.

KU KARANTA: Zaben 2020: An saka dokar ta baci a jihar Amurka

Shugaba Trump ya na banbami, ya ce wasu sun yi zabe bayan lokaci ya kure
Shugaba Trump da Biden Hoto: www.post-gazette.com
Asali: UGC

Shugaba Trump ya yi alkawarin cewa zai fito ya yi wa mutanen kasar Amurka jawabi na musamman game da sakamakon zaben da ake yi.

Kafin yanzu, Trump ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta na kan nasara a zaben Amurkan. Shugaban kasar ya gode wa jama’an da su ka kada masa kuri’a.

A baya kun ji cewa Shugaba Amurka, Donald Trump ya ji dadin gangamin da wasu Bayin Allah su ka shirya masa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A shafin Twitter, Trump ya tanka Magoya-bayan na sa daga uwa-Duniya, Ontisha a jihar Anambra

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng