Zaben Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon

Zaben Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon

- A yau, Talata, uku ga watan Nuwamba ake gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a kasar Amurka

- Amurkawa na da zabin kada kuri'a ga daya daga cikin 'yan takara guda biyu; Donald Trump da Sanata Joe Biden

- Trump ya na takara ne a karkashin inuwar jam'iyyar 'Republican' yayin da Biden ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar 'Democrat'

A ranar Litinin ne Charlie Baker, gwamnan jihar Massachusetts da ke kasar Amurka, ya bukaci wasu jami'an tsaro na musamman guda 1,000 a kan su kasance cikin shirin ko ta kwana koda za a samu hargitsi a zaben kasar ranar Talata.

A jihar Oregon kuwa, gwamna Kate Brown ta saka dokar ta baci a yankin Portland bisa tunanin samun yiwuwar barkewar rikici sakamakon zaben da ake gudanarwa ranar Talata, kamar yadda Punch ta rawaito.

A karkashin dokar ta bacin, rundunar 'yan sandan jihar Oregon da babban jami'in tsaro na yankin Multnomah zasu tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jama'a a Portland.

KARANTA: 'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka

Gwamna Brown ta sanar da cewa ta umarci jami'an tsaro na musamman masu kwarewa wajen sarrafa jama'a su kasance cikin shiri.

"Mun san akwai batagarin mutanen da zasu fake da zanga-zangar lumana a daren ranar zabe domin tafka barna da lalata dukiya, ba zamu yarda da hakan ba," kamar yadda Brown ta fada ranar Litinin.

Zaben Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon
Trump a Michigan
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa shugaban ƙasa Donald Trump ya jaddada cewa zai sake kafa tarihi a yayin da Amurkawa ke jefa ƙuri'un su a ranar Talata.

KARANTA: kuɗin ceto: FG ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i

A ranar Litinin ne Trump ya kammala rufe yaƙin nenan zaɓensa a cikin ɗumbin cikowar jama'a a jihohi huɗu na Amurka.

Trump ya nanata maganar aringizon ƙuri'u da aka yi masa.

Ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a gaban jama'a da safiyar ranar Talata a Grand Rapids, Michigan, in zaku tuna, nan ne wurin da Trump ya kammala yaƙin neman zaɓensa a shekarar 2016.

Trump mai shekaru 74 ɗan takarar jam'iyyar Republican ya ce zai sake komawa a karo na biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel