‘An karrama ni’- Trump ya yi godiya ga wadanda su ka fito nuna goyon-baya
- Donald Trump ya ce wani abu game da gangamin da aka shirya masa a Najeriya
- Wasu mutanen garin Onitsha, jihar Anambra sun fito su na goyon-bayan Trump
- Shugaban kasar ya nuna ya ji dadin wannan karrama wa da aka yi masa a Afrika
Donald J. Trump, shugaban kasar Amuka kuma ‘dan takarar jam’iyyar Republican a zaben da ake yi, ya waiwayi Najeriya a ranar 3 ga wata Nuwamba, 2020.
Shugaba Donald J. Trump ya yi magana game da gangami da wasu mutanen Najeriya su ka shirya domin nuna goyon-baya gare shi a zaben da ake yi a Amurka.
An dauki bidiyon wadannan Bayin Allah da su ka fito su na nuna wa shugaban Amurkan goyon-baya tun daga jihar Anambra a Kudu maso gabashin Najeriya.
KU KARANTA: Biden zai doke Trump - Hasashe
Wani mutumi mai suna Mista Abraham Opeyemi ya fara wallafa wannan bidiyo a shafinsa. Daga baya Trump ya sake wallafa bidiyon a Twitter a jiya da yamma.
Jaridar The Cable ta ce an yi wannan gangami ne a garin Onitsha, inda jama’a su ka fito da tutoci da kuma takardu da ke nuna goyon-bayan Donald Trump.
Za a ga masu tattakin da takardu su na “Make America Great Again”, “President Trump: America Needs A Man Like You”.
Abraham Opeyemi mutumin jihar Ondo ne, kuma Fasto a wani babban coci da ke garin Akure.
KU KARANTA: Abubuwan da za su ba Trump nasara a Amurka
Trump ya rubuta a Twitter: “Gangamin da aka shirya mani a Najeriya, an karrama ni sosai.”
Ko da iyakar abin da shugaban mai neman tazarce ya rubuta kenan, sakon na sa ya samu karbuwa inda sama da mutum miliyan 10 su ka kalli bidiyon zuwa yau.
Jaridar New York Post ta ce akalla 58% na mutanen Najeriya su ke kaunar Donald Trump. Akwai asalin‘Yan Najeriya fiye da 300, 000 da aka haifa a Amurka.
Kawo yanzu a zaben Amurkan, Trump ya kawo Jihohi 13, shi kuma Biden ya yi galaba a Jihohi 11.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng