Kiyasi 10 dake nuna Donald Trump zai lashe zaben yau

Kiyasi 10 dake nuna Donald Trump zai lashe zaben yau

Bayan kimanin shekaru hudu a ofis a matsayin shugaban kasar Amurka, Donlad Trump, na bukatan yan kasar su sake zabensa karo na biyu a zaben dake gudana yau.

Babban abokin hamayyarsa a zaben da ke gudana yanzu haka shine dan takaran jam'iyyar Democrat, Joe Biden.

Legit.ng ta zakulo muku wasu kiyase-kiyase 10 da dake nunawa Donald Trump zai lashe zaben kamar yadda CrowdWisdom360 ya bayyana.

1. Halloween Mask Sale

Kamfanin Halloween Mask Sale ya shahara da kiyasin wanda zai yi nasara a zaben Amurka tun shekarar 1984

A wannan karon, ya yi kiyasin cewa bisa ga adadin wadanda suka sayi rigar fuska a bana, Trump ya kayar da Biden.

2. Robert Cahaly

Cahaly, tsphon shugaban Trafalgar, ya alanta cewa Trump zai lashe zaben amma ta kwalejin zabe kamar yadda yayi a 2016.

Yace: "Akwai wasu kuri'u boyayyu jama'a,"

3. Helmut Norpoth

Dogaro kan sakamakon zaben fidda gwani, Norrpoth ya bayyana cewa shugaba Trump zai lashe zaben.

4. Binciken kamfanin Pew

Wani shahrarren kamfanin bincike, Pew, ya alanta cewa Trump na da daman lashe zabe da maki 50%, yayinda Biden ke da 48%.

5. Kiyasin Jeffrey Gundlach

Bayan dade da kiyasin zaben 2016, shahrarren attajirin ya c Trump zai sake nasara

KU DUBA:An kwace zanga-zangar EndSARS ne don raba Najeriya - Shugabannin Arewa

Kiyasi 10 dake nuna Donald Trump zai lashe zaben yau
Kiyasi 10 dake nuna Donald Trump zai lashe zaben yau Hoto: @realDonaldtrump
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata

6. Mitt Romney

Duk da cewa dan adawan Trump ne, Mitt Romney ya bayyana cewa Shugaba Trump zai doke abokin hamayyarsa, saboda karfin mulki.

7. Nigel Farage

Dan siyasan kasar Ingila, Nigel Farage, ya ce: "Ina mai tabbatar muku da cewa Donald Trump zai lashe zaben 3 ga Nuwamba, 2020."

8. Farfesa Bela Stantic

Ta hanyar amfani da bayanan dandalin sada zumunta, Farfesa Bela ya ce Trump ya tsallaka rijiya da baya kuma zai ci.

9. Steve Moore

A matsayin mabiyi bayan Trump kuma masani tattalin arziki, ya ce shugaban kasan zai lashe zaben saboda mutane na gudun hijra daga jihohin Democrats irinsu New York, Illinois, California, da Pennsylvania .

10. Arch Crawford

Masani ilmin taurari, Crawford, ya ce Trump zai kayar da Joe Biden kamar yadda ya lallasa Clinton a 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng