Rahotanni: Biden ya sha gaban Shugaban kasar Amurka Trump a zaben 2020

Rahotanni: Biden ya sha gaban Shugaban kasar Amurka Trump a zaben 2020

- Rahotanni su na cewa Democrats na kan gaba a zaben da ake yi a Amurka

- Masu bibiyar zaben Amurkan su na ganin Donald J. Trump zai sha kashi

- An yi irin wannan hasashe a zaben 2016, amma Trump ya kowa mamaki

Punch ta ce alkaluma sun nuna ‘dan takarar jam’iyyar hamayya, Joe Biden zai yi galaba a kan Donald J. Trump a zaben shugaban kasar Amurka.

A ranar Talata mutanen Amurka za su san matsayarsu, bayan an yi yakin-neman zabe inda Donald Trump da kuma Joe Biden su ka gwabza.

Rahotanni daga AFP sun bayyana cewa farin-jinin Joe Biden ya karu da 7.2% a ranar Asabar.

Wannan ya sa ake ba ‘dan takarar adawa nasara. Hasashe ya nuna Donald Trump ba zai yi nasara ba, rabon da shugaban kasa ya fadi zabe tun 1993.

KU KARANTA: An sace N700m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka

Sai dai an yi irin wannan a 2016 inda mafi yawan masu hasashe da fashin bakin siyasa su ka ba Democrats nasara, amma a karshe Trump ya lashe zabe.

An dauki tsawon lokaci alkaluma su na nuna cewa da wuya Donald Trump ya kai labari. Nan da ‘yan kwanaki kadan za a tabbatar da gaskiyar lamarin.

International News ta ce alkaluma sun nuna mata Joe Biden ya na da damar 51% na lashe zaben, yayin da shugaba Donald Trump ya ke da damar 43%.

An yi amfani ne da hasashen karshe da aka yi tsakanin rana 27 zuwa 29 na watan Oktoban jiya.

Rahotanni: Biden ya sha gaban Shugaban kasar Amurka Trump a zaben 2020
George HW Bush ya sha kashi a zaben 1993 Hoto: www.usatoday.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Abubuwa 5 da za su sa Biden ya doke Trump a zaben 2020

Shugaba mai-ci Donald Trump ya na bin Joe Biden kan-kan-kan a sauran kuri’un ‘Electoral College’, da za su sake ba shi damar nasara a zaben.

Reuters/Ipsos ta ce za a fafata a jihohi irinsu Florida, North Carolina, da Arizona. CNN ta na ganin Joe Biden ya sha gaban Trump a wadannan yankuna.

Axios ta fitar da rahoto cewa Trump zai ba kansa nasara muddin ya ga ya na kan gaba da zarar an fara fito da kuri’u, shugaban kasar ya musanya wannan.

A kwanakin baya an tafka muhawara tsakanin Donald Trump da Joe Biden yayin da 'yan takarar biyu su ke neman mulkin kasar Amurka a zaben bana.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya kira Trump ‘Makaryaci’ a muhawarar ta su ta farko.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel