Fato Sandi: Allah ya maka sakayya da gidan Aljannah - Shettima ga Zulum

Fato Sandi: Allah ya maka sakayya da gidan Aljannah - Shettima ga Zulum

- Sanata Kashim Shettima ya yabawa gwamnatin Babagana Umara Zulum

- Tsohon gwamnan ya yarda cewa gwamnatin Magajinsa ta na aiki a Borno

- Gwamna Babagana Umara Zulum ya karasa wani aiki da aka bari a jihar

Ganin yadda gwamna Babagana Umara Zulum ya ke aiki babu kama hannun yaro a jihar Borno, tsohon gwamnan Jihar, Kashim Shettima ya fito gaban Duniya ya jinjina masa.

Kashim Shettima wanda ya sauka daga kan mulki a 2019 ya ji dadin yadda Magajinsa watau Farfesa Babagana Umara Zulum ya cigaba da aikin da gwamnatin baya ta bari.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa dorawa kan ginin da aka yi a baya shi ne kashin bayan duk wani tsari da gwamnati za ta kawo, don haka ya yi wa gwamnan addu’a.

“Cigaba da aikin baya ya na da tasiri wajen nasarar duk wani tsare-tsare, sannan Madaukakin Sarki Allah ya yi wa Babagana Umara Zulum albarka, ya ba shi Aljannar Firdausi.”

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Shettima ya kara da cewa: “Wannan makarantar firamaren Fato Sandi ce, na tafi na bari an yi kashi 75% na aikin gininta, kuma Mai gidana gwamna Zulum ya kammala aikin.”

Bayan ya kira Magajin na sa da mai gidansa, Kashim Shettima ya bayyana cewa yanzu ana shirin kaddamar da wannan makaranta firamare da gwamnatinsa da ta Zulum ta gina.

Sanata Shettima ya na ganin cewa da wannan, babu shakka gwamnatin Borno ta na kokari. A lokacin da Shettima ya bar ofis, ya kammala kashi uku cikin hudu na wannan aiki.

Kusan dai tsohon gwamna Shettima ne ya zakulo Babagana Zulum a matsayin magajinsa. Kafin nan Zulum ya rike mukamai a gwamnatin Shettima, kuma ya nuna rikon amana.

Sanatan na yankin Borno ta tsakiya mai-ci ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na tuwita, @KashimSM da kimanin karfe 6:45 na yammacin ranar Asabar, 6 ga watan Yuni, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel