Alheran Gwamna Babagana Zulum daga bakin Abdallah Gadon-Kaya

Alheran Gwamna Babagana Zulum daga bakin Abdallah Gadon-Kaya

- Abdallah Usman Gadon-Kaya ya fito ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno

- Malamin ya ce irinsu Farfesa Babagana Zulum ake bukata su fito takara

- Shehin ya yabi Gwamnan da tsoron Allah da kirki, da kaunar Talakawa

Babban malamin addinin musulunci, Dr. Abdallah Usman Gadon-Kaya, ya yi magana game da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

A wajen wani karatu da Abdallah Usman Gadon-Kaya ya ke yi, ya lissafo alheran gwamnan Borno, ya ce irinsa su ka dace su rike mulkin Najeriya.

Malamin ya ke cewa a wannan marra, babu gwamna da aka yi na kirki irin Farfesa Umara Zulum.

Ya ce: “Allah ya saka wa gwamnan Borno da alheri, a cikin gwamnonin Arewa ko na Najeriya wadanda mu ka sani, Allah bai yi wani gwamna irinsa ba a kwanan nan."

KU KARANTA: Jama'a su na wahala a yau - Sheikh Goro Dutse

“Alheransa sun bayyana, mutuncinsa ya bayyana, tsoron Allah na sa ya bayyana.” Inji Shehin.

Ya ce akwai wani na-kusa da gwamnan da ya shaida masa duk ranar Litinin da Alhamis, sai Zulum ya yi azumin nafila, wanda ya na cikin manyan ibadun nafila.

Bayan haka, Malamin ya ce Farfesa Zulum ya kan sha ruwa ne a kowace Litinin idan ya kai azumi a gaban mahaifiyarsa, duk da ya na rike da kujerar gwamna.

Shehin ya tunawa jama’a irin kokarin gwamnan na ganin mutane sun sauke nauyinsu. Ya ce: “Karfe 7:00 za ka gan shi ya fito, ya na bibiyar mutane ko an fito aiki.”

KU KARANTA: Oshiomhole ya na so ya sasanta da Gwamnan Benuwai a wajen kotu

Alheran Gwamna Babaganda Zulum daga bakin Abdallah Gadon-Kaya
Gwamna Babaganda Zulum Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abdallah Usman Gadon-Kaya ya ce a karkashin mulkin Zulum wanda ya karbi mulki a shekarar 2015, “Mutanen Maiduguri, sun samu saiti.”

“A inda ake rikici, kokari ya ke ta yi, ya gina masu gidaje su koma. A da kuwa duk sun dawo sun cika gari, su na bara.” Ya ce gwamnan ya kan yi wa talakawan rakiya.

Malamin ya bada labarin irin kundubalar da gwamnan ya yi kwanaki, ya ce don haka irinsu ake nema su fito takara a Najeriya, mutane su kada masa kuri’a.

Dazu kun ji cewa Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta samu taimako sosai wajen kafa Jami’ar addinin musulunci a jihar Jigawa.

Sheikh Bala Lau ya ce sun samu gudumuwar kudi har daga wajen wadanda ba Musulmai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel