Fasto Adeboye, Tsohon Gwamna Dickson da Gwamna Diri sun hadu a Bayelsa

Fasto Adeboye, Tsohon Gwamna Dickson da Gwamna Diri sun hadu a Bayelsa

- Douye Diri ya ce Enoch Adeboye ya yi masa addu’a wajen zama Gwamna

- Diri ya dare kujerar Gwamna ne yayin da APC ta ke shirin hawa kan mulki

- Fasto Enoch Adeboye Mai gidan Farfesa Yemi Osinbajo ne a cocin RCCG

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya bada labarin yadda mukaddamin cocin darikar RCCG, Enoch Adeboye ya yi masa albashir da zama gwamna.

Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa Fasto Enoch Adeboye ya shaida masa zai karbe nasararsa a kotu, sannan ya dawo ya rike kujerar gwamnan Bayelsa.

Jaridar Punch ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani taron ibada da cocin RCCG ya shirya a ranar Juma’ar da ta wuce, 30 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Gwamnan Edo ya roki Jami'an 'Yan Sanda su koma bakin-aiki

Da ya ke bada labarin abin da ya faru da shi, ya ce bai amince da sakamakon zaben gwamnan Bayelsa da aka yi ba, Diri ya ce don haka ya kai kara kotu.

Douye Diri ya ce a wannan lokaci da ake jiran shari’ar kotu, ya kai wa Fasto Enoch Adeboye ziyara, inda ya yi masa addu’a, ya roko masa sa’ar Ubangiji.

Babban shehi, Enoch Adeboye, ya fada wa Sanata Diri ya je ya karbo nasararsa a gaban kotu, daga baya ya dawo coci ya yi godiya ga Ubangiji, haka kuma aka yi.

A cewar Diri: “Na ziyarci cocinsa a ranar 11 ga watan Disamba a lokacin da ake wani shiri na ‘Great Turn Around’”

Fasto Adeboye, Tsohon Gwamna Dickson da Gwamna Diri sun hadu a Bayelsa
Douye Diri Hoto: www.legit.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnoni, Sarakuna, Ministoci sun yi taro a Kaduna

“Bayan an kammala ibada, sai na je na ga Daddy G.O. ya yi mani addu’a, bayan nan ya fadi mani cewa ‘Ta gyaru, ka je idan ka karbo mulki, ka dawo cocin.”

Haka aka cika ba da shari’a, Douye Diri ya ce a ranar 14 ga watan Fubrairu, ana saura sa’a 24 a rantsar da gwamna, kotu ta tabbatar da nasararsa a kan APC.

“Ina so in gode wa Daddy G.O, da wadanda su ka yi mani addu’a. Yau ni ne gwamnan Bayelsa.” Tsohon gwamna Seriake Dikson ya halarci wannan taron ibada.

Idan mu ka koma kasar waje za mu ji cewa a zaben Amurka, ana hasashen Joe Biden ya yi gaba, yayin da Donald Trump ya ke barazanar ba kan shi nasara.

Hasashen da ake yi ya nuna alamun shugaban kasa Donald Trump ba zai zarce kan mulki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel