Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo

Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo

- Jarumin Kannywood, Mallam Ibrahim Sharukhan ya aika budaddiyar wasika zuwa ga Rahama Sadau

- Sharukhan ya yi Allah-wadai da shiga ta nuna tsaraici da jarumar tayi a wani hoto da ta wallafa a shafukanta na sadarwa

- Ya kuma jaddada cewa su yan Kannywood basa tare da ita a kan wannan abu da take yi

Shahararren jarumin masana’antar Kannywood, Mallam Ibrahim Sharukhan ya yi Allah-wadai da hoton abokiyar sana’arsa Rahama Sadau, wanda ta saka kaya da ke nuna waani bangare na jikinta.

A wani bidiyo da jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana cewa su yan Kannywood da musulmin duniya basa tare da Rahama a cikin abinda ta aikata wanda ya janyo har wani ya yi batanci ga manzon Allah (SAW).

Sharukhan ya jaddada cewa duniya makaranta ce wanda bai shigo cikinta ba tana jiransa. Ya kuma bayyana abunda jarumar tayi a matsayin rashin tarbiya daga iyaye.

KU KARANTA KUMA: Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce

Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo
Ibrahim Sharukan ya yi zazzafan martani a kan hoton Rahama Sadau, bidiyo Hoto: Rahama Sadau/Malam Ibarahim Sharukhan
Asali: Instagram

A cikin biyon nasa, an jiyo yana fadin cewa: “Sunana Ibrahim Sharukhan masoyin Annabi a koda yaushe, da kakkausar murya zuwa ga Rahama Sadau jaruma a Kannywood, bama tare da ita game da wannan abun da take yi na batanci ake koyi da ita, don haka abunda tayi shiga ta rashin mutunci har ta janyo aka yi wa addinin Musulunci batanci mu yan Kannywood bama tare da ita.

“Sannan kuma ina sanar da iyayenta wadanda suka haife ta idan ba za su fada mata gaskiya ba, toh mu ta zo inda za a fada mata gaskiya tunda tana tare damu a sana’armu. Ko ni na sa ta a fim kuma na biyata don haka ina da hurumin da zan iya cewa bama tare da ita

“Sannan ina sanar da yan Kaduna dukkan jarumi ko jaruma wanda zai janyo batanci ga addinin Musulunci su dauki mataki da kansu. Mu a nan Kano akwai wani da yayi batanci ga addini aka je har gidansu aka ragargaza shi sannan shi ya gudu ya bar garin.

KU KARANTA KUMA: An shiga halin fargaba yayinda wata bakuwar cuta ta kashe mutane 15 a Jihar Delta

"Don haka in tayi wannan abu ba iya Kannywood tayi mawa ba, dukkan Musulmi gaba daya tayi mawa. Sannan bata da tunani kuma iyayenta basu da tunani, tunda tana da kanne mata, wa zai je gidansu ya auri mace tunda su yan Allah-wadai ne."

A gefe guda, babban daraktan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Falalu Dorayi, ya yi martani a kan shigar nuna tsaraici da jarumar masana’antar, Rahama Sadau ta yi.

A wata wallafa da yayi a shafin Instagram ya ja hankali a kan illar da ke tattare da shigar tsaraici ga mace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng