Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi

Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi

- Falalu Dorayi ya yi tsokaci a kan shigar Rahama Sadau da ya janyo cece-kuce

- Babban daraktan na Kannywood ya ce ba daidai bane mutum yaa yi shiru a yayinda ya ga dan uwansa yana aikata barna

- Ya yi korafi a kan yadda dabi’ar shigar banza ke neman zama ruwan dare a a tsakanin Al’umma

Babban daraktan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Falalu Dorayi, ya yi martani a kan shigar nuna tsaraici da jarumar masana’antar, Rahama Sadau ta yi.

A wata wallafa da yayi a shafin Instagram ya ja hankali a kan illar da ke tattare da shigar tsaraici ga mace.

KU KARANTA KUMA: Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi

Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama sadau shagube a kan shigar da ta yi
Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama sadau shagube a kan shigar da ta yi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya ce: “Yin barna ko yadata ko wacce iri ce Bana goyan bayanta. Lallai shigar tsiraici ga mace musulma, sharri ne mai girma gareta, da kuma Al’ummar da take cikinsu. Kuma shigar zubar da mutuncin family din ta ne.

“Rashin Magana akan wannan yana daidai da kace a cigaba da aikatawa. Ita kuma Uqubar Allah in ta tashi zuwa zata shafi kowa ne. Allah ya shirye mu.

“Nasiha da jan hankali ba da tozarci ba. Itace hanya mafi kyau musulmi yaiwa Dan uwansa musulmi Nasiha, akan wata barna da yaga yana aikatawa.

“Ita dai Dabi’ar shigar banza nema take ta zama ruwan dare a Al’ummarmu. Abu ne da yake faruwa a rayuwar Yau da kullum, mu duba gidajen biki, Gidan suna, tarurruka, makarantun mu tun daga primary zaka wasu yara mata na tafiya kansu babu DANKWALI sai gashin kansu a daure, ballantana aje secondary ko Universities, Duk wadannan suna faruwa a gaban IYAYE, MALAMAI, YAYYE, KAWUNNAI.

KU KARANTA KUMA: An shiga halin fargaba yayinda wata bakuwar cuta ta kashe mutane 15 a Jihar Delta

“Mace tana da daraja gyaruwarta gyaruwar Al’umma ne, mu tashi tsaye akan nusar dasu kunyar su da mutunci su. Domin gyaran ‘Yayanmu masu zuwa a gaba.

“Rasulullah Annabi (S.A.W) Yace “Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku za a tambaye shi game da abin da aka bashi kiwo”.

“Kofar tuba a bude take da duk wanda yai kuskure, gaggawar Istighfari yafi Jinkirin yinsa. dukkan mu masu laifi ne, Allah ne yake rufa namu asirin. A cigaba da addu’ar neman gafarar Allah

“A KARSHE Ga Hadisin Annabin tsaira (S.A.W) akan masu FIDDA TSIRAICI Yace; "A karshen zamani za’a samu wasu mata ga tufafi a jikinsu amma tsurara suke, tufafin bai rufe tsiraicin suba."

"RASULULLAH (SAW) Yace; “A TSINE musu, domin su din TSINANNUNE." RASULULLAH (SAW) Yace; "Wallhi ko Kamshin ALJANNA baza su ji ba." Allah ka shiryamu da zuriarmu da dukkan musulmi baki daya.

“Wajibine Mazan da Matanmu mu tashi mu yaki Shaidan La’anannen Allah, Yadda baibar Uban Talikai Annabi Adamu ba, haka muma bazai bar mu ba. Yakinsa kullum shine yasa mu kauce hanyar Allah mubi tasa batacciya.

“Allah ya shiryemu baki daya ya tsare mu biyewa son zuciyarmu. Amin."

A baya mun ji cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta saki wasu zafafan hotunanta a shafin sadarwa ta Intagram.

Jarumar ta kasance cikin ado da walwali inda ta sanya doguwar riga na gani da fada.

Sai dai a daya daga cikin hotunan da jarumar ta wallafa a shafin nata, an gano yadda aka bude bayan doguwar rigar wato ma’ana dukka bayanta ya kasance a waje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel