Muhimman abubuwa 5 da za su iya saka Trump shan kaye a zaɓen shugaba ƙasa na 2020

Muhimman abubuwa 5 da za su iya saka Trump shan kaye a zaɓen shugaba ƙasa na 2020

- A ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba miliyoyin Amurkawa za su fita don zaben shugaban da zai mulke su daga 2020 zuwa 2024

- Manyan wadanda za su fafata a zaɓen su ne Shugaba Donald Trump da na jam'iyyar Republicans da Joe Biden na Democrats

Duk da cewa Shugaba Trump shi ke kan mulki, Legit.ng ta yi nazari kan wasu muhimman abubuwa biyar da ka iya sa shi faɗi zaben.

1. Yadda ya tafiyar da annobar korona

Irin yadda Shugaba Trump ya tunkari annobar korona na ɗaya daga cikin abubuwan da ka iya saka shi faɗi zabe.

Annobar ta yi tasiri sosai inda kimanin mutum miliyan 9 suka kamu fiye da 200,000 suka rasu a cewar alƙalluma daga Worldometre.

Amurkawa da dama na ɗora laifi kan Trump duba da cewa bai ɗauki matakai daƙile annobar ba da farko.

Abubuwa hudu da za su iya saka Trump shan kaye a zaben 2020
Abubuwa hudu da za su iya saka Trump shan kaye a zaben 2020
Asali: UGC

2. Muhawarar ƴan takarar shugaban kasa

A cewar kafar watsa labarai ta BBC, irin yadda Trump ya rika katsa abokin muhawararsa idan yana magana bai haifa masa ɗa mai ido ba.

Kafar watsa labaran na Birtaniya ta ce salon ya janyo masa baƙin jini wurin mata da ke garuruwan gefen birane da sune kowanne ɗan takara ke neman ƙuri'unsu.

3. Zaɓukan jin ra'ayin al'umma sun nuna magoya bayan su sun rayu

Duk da cewa ya shafe kimanin shekaru hudu a kan mulki har yanzu Trump na bayan Joe Biden a cewar manyan alƙalluman jin ra'ayin mutanen ƙasar.

BBC ta ruwaito cewa masu nazarin zaɓe suna da ƙara hasashen Trump ba zai zarce ba.

Legit.ng ta tattaro cewa shafin Nate Silver ta Fivethirtyeight.com a yanzu ta ce Biden na gaba da 87% yayin da Decision HQ ita kuma 83.5%.

DUBA WANNAN: Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno

4. Karayar gwiwa daga wasu ƴan Republicans

Wasu manyan mambobin jam'iyyar su Trump ta Republicans sun nuna fargabar suna iya faɗi zabe a cewar The Guardian UK.

Misali, an ruwaito Sanatan Republican Ted Cruzb yana cewa:

"Ina ganin zaɓen tana iya zama mai wahala. Za mu iya rasa White House da Majalisar, zai iya zama gwagwarmaya mai kama da Watergate."

KU KARANTA: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

5. Kalon mai nuna banbancin launin fata da ake yi wa Trump

Duk da cewa Trump ya sha furta cewa 'babu wanda ya kai shi rashin nuna banbancin launin fata," ayyukan da ya ke aikatawa sun saɓa da hakan.

A 2019, The Time ta ruwaito cewa wasu ƴan Republicans sun yi imanin cewa 'harin nuna banbancin launin fata' da Trump ke yi za su kawo masa cikas a zaɓen 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel