Joe Biden ya kira Donald Trump ‘Makaryaci’ a muhawarar zaben kasar Amurka
- An tafka muhawara tsakanin Shugaba Donald Trump da Joe Biden a Amurka
- ‘Yan takarar na zaben Amurka sun yi haduwarsu ta farko a ranar Larabar nan
Muhawarar shugaba Donald Trump da abokin hamayyarsa, Joe Biden bai yi kyau ba, yayin da manyan ‘yan siyasar su ka shafe sa’a guda da rabi da juna a jiya.
A wannan muhawara wanda ita ce ta farko tsakanin ‘yan takarar zaben shugaban kasar na Amurka, an rika sakin layi, aka koma yi wa juna cin mutunci da ba’a.
Masu hasashen siyasar kasar wajen sun yi tunanin cewa Donald Trump ne zai dura kan Joe Biden, sai dai kusan akasin hakan ne ya faru a daren ranar Laraban.
Yayin da ake wata magana, ‘dan takarar jam’iyyar Democrat din ya kira abokin adawarsa na Republican watau shugaban kasa Donald Trump da makaryaci.
KU KARANTA: Abin da zai faru idan Biden ya samu mulki – Trump
“Duk abin da ya ke cewa karya ce kurum, ban zo nan da nufin bankado karyarsa ba.” Inji Biden.
Haka zalika Joe Biden ya kira shugaban na Amurka da mashiririci. ‘Dan takarar ya ke cewa: “Zai yi wahala ka iya cewa wani abu tare da wannan mashiriricin.”
Akwai kuma lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya fadawa Trump, “Wannan mutumi ba za ka yi mana shiru ba?” Har an fara yi wa Trump ba’a da wannan.
Shi ma Donald Trump ba a bar sa a baya ba, domin kuwa ya caccaki Biden a wasu wuraren. Trump ya nuna Biden dakiki ne bayan ya soki wasu matakai da ya dauka.
KU KARANTA: COVID-19 ta kashe Mutumiyar Amurka a otel a Najeriya
“Ko dai kai ne na kashin-baya a ajinku, ko kuma na kusa da haka.” Trump ya ragargaji Biden.
A wasu lokutan kuma Trump ya shiga sukar iyalin Biden da zarginsu da badakala, ya ce an kori Hunter Biden daga gidan soja ne a dalilin masifar shan kwayar da ya ke yi.
A wajen, Biden ya ce Amurka ba ta taba yin shugaban kasa na banza irin Donald Trump ba.
Za ku tuna cewa kasar Amurka ta makawa wasu ƴan Najeriya takunkumin shiga kasarta saboda munannan rawar da suka taka yayin zaben gwamna da aka yi a wasu jihohi.
Amurka haramtawa wasu manyan 'yan Najeriya shiga kasar ne domin gyara zabe a Najeriya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng