2023: Kungiya ta yi barazanar yin ƙarar El-Rufai a kotu idan ya ki fitowa takarar shugaban kasa

2023: Kungiya ta yi barazanar yin ƙarar El-Rufai a kotu idan ya ki fitowa takarar shugaban kasa

- Wata kungiya ta yi barazanar yin karar El-Rufai har kotun koli don tilasta shi tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

- Babuga, shugaban kungiyar ta Nasiriyya ya ce babu wanda ya fi El-Rufai dacewa da shugabancin Najeriya a 2023

-Ya bukaci dattijan Arewa da su saka baki domin ganin El-Rufai ya amince da tsayawa takara a shekarar ta 2023

Kungiyar Nasiriyya a jihohi 21 sun bayyana aniyarsu ta janyo gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa a babben Zaben 2023.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna, shugaban kungiyar Nasiriyya kuma mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso yamma, Dr. Garkuwa Ibrahim Babuga, ya ce tuni shirye shirye sun yi nisa na shigar da karar El-Rufai kan kalaman sa nacewa bashi da sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Zaben 2023: Kungiyoyi a jihohi 21 sun bukaci El-Rufai ya tsaya takara
Zaben 2023: Kungiyoyi a jihohi 21 sun bukaci El-Rufai ya tsaya takara. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Babuga Ya ce basu da matakin da yafi zuwa Kotu saboda sunyi magana da gwamnan akan maganar amma yayi watsi da bukatar su kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

"A shirye muke muje har kotun koli," A cewarsa.

DUBA WANNAN: Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci da aka yi ga Manzon Allah

"Munyi magana da iyayensa da wasu yan uwansa amma bamu samu gamsasshiyar amsa ba.

Dole kuto za Mu je. Najeriya ta El-Rufai ce 2023. El-Rufai ya cancanci ya zama shugaban kasa duba da irin aikin da yake yi.

"Mutane da dama sun bukaci El-Rufai ya tsaya takara. Ban san wani irin kira yake so a masa ba, Kun dai ga irin ci gaban da ya yi a birnin tarayya Abuja da kuma jahar Kaduna. Shi yafi cancanta da fadar Aso Rock a 2023.

"Mu ci gaba da biyayya da goyawa Shugaba Buhari baya ya karasa wa'adinsa. Amma El-Rufai a matsayin shugaban kasa kuma magajin Buhari zai kara hada kan yan Najeriya.

"Muna kira ga dittijan Arewa, da suyi watsi da bambancin jam'iyya, mu hada karfi da kuma gangami don El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa.

KU KARANTA: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

"Duk da cewa bai Amsa kiran mu ba, za muje Kotu don tilastawa El-Rufai ya nemi kujerar takarar shugabancin Najeriya.

"Zamu shiga Kotu ranar 2 ga watan Nuwamba, 2020, za muje kotu mai lamba 13 a nan Kaduna. Lauyan mu shine Barista El- Zubair," a fadarsa.

Akan batun gwamnan da yayi a kafafen sadarwa cewa yana goyon bayan shugaban kasa Ya fito daga yankin Kudu a Zaben 2023, shugaban kungiyar Nasiriyyar Ya ce wannan shi ne ra'ayin El-Rufai a halin yanzu.

"Ra'ayinsa ne. Yanzu kokarin mu shine muga mun jawo cikin masu neman kujerar. El-Rufai zai zama shugaban Najeriya mafi daraja a 2023 da yardar Allah," A cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel