Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi

Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi

- Sheikh Abdul Rahman Sudais na kasar Sadiyya, yi tir da mutanen da ke batanci ga Annabi Muhammadu

- Limamin na Masallacin Harami ya bayyana masu irin wannan halayya a matsayin kastantattu marasa mutunci

- Ya kuma gargadi masu aibata janibin Manzon Allah da su kiyaye, su guji fushin Ubangiji da fitinar da za ta iya afka musu

Babban limamin Masallaci kasa mai tsarki, Sheikh Abdul Rahman Sudais, ya yi Allah-wadai da wadanda suka yi batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Sheikh Sudais, wanda ya kasance ministan Masallatai na kasar Saudiyya a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, ya nuna rashin jin dadi tare da yin kakkausar lafazi a kan masu aibata Annabi.

Shehin Malamin ya bayyana masu irin wannan danyen aiki a matsayin kaskantattun mutane marasa daraja da kima, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna

Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi
Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi Hoto: The International News
Asali: UGC

Ya ambato kyawawan halaye da dabi’un Annabi, yana mai bayyana shi da amintacce, karimi, mai saukin hali wanda duniya ta cika da sanin daraja da matsayinsa.

A karshen hudubar, Sudais ya ja kunnen masu afka wa janibin Manzon Allah da su kiyaye, su guji fushin Allah da fitinar da za ta iya afka musu ko azaba mai radadi.

Sheikh Sudais ya rufe da addu’o’in neman zaman lafiya a kasashen Musulmi da duniya baki daya.

KU KARANTA KUMA: Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

A gefe guda, an cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Fathi Hammad, shugaba a ƙungiyar Hamas daga Jabalia ya yi kira ga wadanda suka fito tattalin su hada kai don tunkaro abinda ya kira "cin zarafi" ga Annabi Muhammad.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng