Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

- Wata mota ta cinna kai cikin Masallacin Ka'aba yayinda ta kwaso gudu

- Lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba, da karfe 10:30 na dare

- Sai dai jami'an tsaro sun yi nasarar damke direban wanda baya a cikin hayyacinsa

Rahotanni sun kawo cewa wata mota ta sanya kai gadan-gadan cikin Masallacin Ka’aba a guje, har ta kai ga gab da kofar shiga cikin masallacin taa 89.

Kakakin gwamnan Makka, Sultan al-Dosari, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito.

An tattaro cewa motar ta kustsa kai cikin farfajiar Sarki Fahd, wanda aka hade da masallacin ta baya.

Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu
Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu @bbchausa
Asali: Twitter

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da ababen kariya sannan ta dangana ga kofar shiga masallacin.

KU KARANTA KUMA: Mun sa kafar yaki da akidun addinin Islama, in ji kasar Faransa

Kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito , majiyoyi da dama sun jaddada cewa motar ta shiga farfajiyar masallacin ne ta kan Titi na 15, wanda ita ce babbar hanyar da ta dangane da cikin Farfajiyar Sarki Fahd da ke Masallacin Harami.

An kuma tattaro cewa babu ko mutum guda da ya jikkata a hatsarin yayinda aka damke direban a nan take. An kuma daure hanayyensa kafin aka tisa keyarsa.

"Motar ta dangana ga kofar ne yayin da ta kwaso mugun gudu a kan daya da cikin titunan da ke kusa da farfajiyar masallacin ta bangaren kudu. Amma kuma babu wanda ya jikkata," in ji Sultan al-Dosari.

Ya ci gaba da fadin cewa: "An cafke direban. Dan Saudiyya ne kuma ba ya cikin hankalinsa. An mika shi wurin masu shigar da kara."

KU KARANTA KUMA: An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS

Shingen da ake sakawa a bakin kofar masallacin ba masu kwari ba ne, abin da ya sa motar ta wancakalar da su kenan, kamar yadda ake iya gani a bidiyon.

Shafin Haramain Sharifain ya ce nisan da ke tsakanin ƙofar da motar ta shiga zuwa cikin masallacin bai fi mita 230 ba.

A wani labarin, an cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel