Tsintar gawar mafarauci a daji ya tada hankulan mazauna Abia
- An tsinci gawar wani mafarauci a cikin dajin Nkwonta, bayan sace wayarsa, bindigar farautansa da kuma babur dinsa da akayi
- Dan uwan mafaraucin ya kai kukansa wurin 'yan sanda inda suka bukaci N20,000 kafin suyi bincike akan kisan
- Dan Uwansa ya nuna damuwarsa ta yadda hatta shugaban Nkwonta ya nuna halin ko-in-kula akan kisan
Hankula sun tashi sakamakon ganin gawar wani mafarauci a Isuikwuato a jihar Abia.
An tsinci gawar Kelechi Ochu mai shekaru 27 dan Umuasua a karamar hukumar Isuikuato wanda ake zargin an kashe shi yana farauta.
An tsinci gawarsa a dajin Nkwonta, inda aka ga babu wayarsa, babur dinsa da bindigar farautarsa.
A yadda labari ya iso mana, wani dan uwan mamacin, Ochuba Lucky ya ce Ochu mafarauci ne mai rijista da gwamnati, kuma dan karamar hukumar Isuikuato, kuma mafarauta na da damar zuwa wuri-wuri don farauta.
Ya nuna damuwarsa akan abinda ya fara da dan uwansa, da kuma yadda shugabannin unguwar Nkwonta suka nuna halin ko-in-kula akan al'amarin.
Ya ce, "mun kwashe kwanaki muna nemansa, sai daga baya muka ji labarin an ga gawarsa a dajin Nkwonta, sai naje na sanar da 'yan sanda, suka bukaci N20,000 daga hannuna kafin su dauki mataki.
"Ni kuma bani da N20,000, kawai sai na nemo mutanen Umuasua muka tafi Nkwonta inda muka tsinci gawarsa, muka tafi gida da ita.
"A gaskiya banji dadin yadda mutanen Nkwonta suka nuna rashin damuwarsu akan al'amarin ba, duk da sanar da mai unguwar da mukayi.
"Ina rokon gwamnati tasa baki kuma tayi bincike akai. Muna bukatar sanin wadanda suka kashe dan uwanmu kuma su fuskanci hukuncin da ya dace dasu," ya fadi hakan cikin alhini.
Da Daily Trust ta tambayi mai Unguwar Nkwonta, ya ce ya san faruwar al'amarin, amma a cikin daji abin ya faru.
Ya ce, "a daji abin ya faru ba a masarauta ta ba."
KU KARANTA: Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu
KU KARANTA: Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida
A wani labari na daban, wani matashi mai shekaru 28 wanda ake zargi da kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa a yankin Kisoro da ke yammacin Uganda, ya mika kansa ga 'yan sanda a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba.
Wanda ake zargin mai suna Gerald Ndikumukiza, mazaunin kauyen Kageyo da ke Busengo a ranar Alhamis da ta gabata, ya kashe matarsa mai shekaru 26 mai suna Maserina Mujawimana.
Ya kashe mahaifinsa mai suna Deogratious Sebitama mai shekaru 80, mahaifiyarsa mai shekaru 75 mai suna Bonconsira Nyiraguhirwa kafin ya kashe kanwar matarsa mai shekaru 20 mai suna Joan Nyiramahoro.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng