Dakarun Soji sun ceci mutane 22 da aka sace a Katsina da Zamfara

Dakarun Soji sun ceci mutane 22 da aka sace a Katsina da Zamfara

- Jami'an Sojoji suna cigaba da samun nasara a jihar Zamfara da Katsina

- A cikin makon nan, dakarun Sojin sun samu nasara kan yan bindiga da masu kawi musu labarin leken asiri

Dakarun rundunar Operation Sahel Sanity dake yaki da yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso yamma sun dakile wani hari kuma sun ceci mutane 22 da aka sace.

Sojojin sun samu kwato makamai da harsasai a farmakin da suka kai jihohin Zamfara da Katsina.

Mukaddashin Diraktan yada labarai, Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a a Gusau.

A cewarsa, dakarun da aka tura Moriki da Jangeru sun samu kira a ranar 13 ga Satumba kuma suka dakile shirin da yan bindiga sukayi na kai hari kauyen Mai-Zuma a karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara.

Ya ce sun samu nasarar hakan ne bayan artabun da suka yi a Kayawa inda yan bindiga suka gudu suka bar baburansu uku.

Onyeuko ya ce a ranar 12, dakarun da aka tura Dandume a Katsina sun ceto yan mata biyu da yan bindiga suka sace ranar 18 ga Agusta.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zaben gwamnan jihar APC sun fara shigowa

Dakarun Soji sun ceci mutane 22 da aka sace a Katsina da Zamfara
Dakarun Soji sun ceci mutane 22 da aka sace a Katsina da Zamfara
Asali: UGC

DUBA NAN: Obaseki na PDP da Ize-Iyamu na APC sun lashe akwatunan zabensu

Janar Bernard ya kara da cewa a ranar 17 ga Satumba, Sojin sun ceto mutane 8 da aka sace a Fankama da Sabon Layi a karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina.

"Dakarun da ke sintiri a Chabas, sun ceci mata 11 da yara a hanyarsu ta zuwa kasuwar Batsari yayinda yan bindiga suka tsaresu a titin Shimfida - Gurbi a jihar Katsina," yace

"A ranar 16 ga Satumba, jami'an da aka tura Faskari sun dake wani mai leken asirin yan bindiga mai suna Isah Indo yayinda yake leken inda Sojoji suke."

A wani labarin daban, Rahotanni da ke fitowa daga karamar hukumar Ikpoba Okah na jihar Edo sun bayyana cewa an harbi wani mutum daya da bindiga a Ologbo.

Da aka tuntube shi game da harbin da aka ce an yi a Ologbo Dukedoom, Enogie, Mai martaba Jason Owen Akenzua ya ce ya ji karar harbin bindiga kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Amma tuntubi DPO na 'yan sanda an fada masa cewa 'yan sanda ne su kayi harbi a lokacin da wurin zaben ya rincabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel